Karin Bayan: Manhajar WhatsApp Ta Dawo Aiki Bayan Daina Aiki
Manhajar WhatsApp ta dawo aiki bayan miliyoyin masu amfani da ita sun koka kan rashin iya tura sakonni da samun sakonni a Najeriya da sauran kasashen duniya.
Manhajar ta dawo aiki ne misalin karfe 10 na safe, sa'o'i biyu bayan daina aiki.
Har yanzu kamfanin Meta, mammalakin WhatsApp bai yi bayani kan abinda ya faru manhajar ta daina aiki ne.
Wannan ba shine karo na farko na manhajar zata samu matsala ba.
Ko a watan Afrilu, WhatsApp ta samu matsala a US, Brazil, Paris, Spain, da Costa Rica, rahoton ChannelsTV.
Sama da mutum bilyan biyu ke amfani da manhajar WhatsApp a fadin duniya kuma itace shafi mafi yawan jama'a na uku bayan Facebook da Youtube.
A cewar Statista, akwai mutum milyan 33 masu amfani da WhatsApp a Najeriya kawo Junairun 2021.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dazu Manhajar tura sakonni ta yanar gizo mallakin kamfanin Meta ya samu matsala a yau Talata, 25 ga watan Oktoba, 2022.
Yan Najeriya masu amfani da manhajar sun koka kan yadda ba sa iya tura sakonni da safiyar nan.
Wannan abu ya faru ne karfe takwas da wasu yan mintuna.
Asali: Legit.ng