Yan Mata 2 Sun Lallasa Gardawa 4 Wajen Gasar Cin Malmalan Sakwara
- An yi gasar rige-rigen cin Dalar Sakwara a jihar Ekiti kuma Mata sun bada mamaki matuka
- Duk da an fi su yawa, yan mata biyu sun kayar da dukka mazajen dake musharaka a gasar
- Al'ummar Jihar Ekiti na alfahari da Sakwara kamar dai yadda Bahaushe ke alfahari da Tuwo
Wani bidiyon gasar cin sakwara ya bayyana a shafukan ra'ayi da sada zumunutar yanar gizo a makon nan.
Gasar da ta auku a jihar Ekiti, yankin Kudu Maso Yammaci Najeriya ya nuna cewa yan mata biyu suka kayar da gardawa hudu wajen rige-rigen cinye dalar Sakwara.
Yadda Bahaushe ke alfahari da Tuwon Masara, haka al'ummar jihar Ekiti ke alfahari da Sakwara.

Asali: Twitter
Cikin kasa da mintuna biyu, yarinyar farko ta tayar da dalar Sakwara har da lashe kwano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga baya yarinyar ta biyu ta jijjige sakwaran ba tare da bata lokaci ba.
Jama'a a soshiyal Midiya sun yi Alla-wadai da wadannan samari da suka bari mata suka kada su a irin wannan gasa.
Kalli bidiyon na EkitiTrends ta daura:
Asali: Legit.ng