An Samu Tashin Hankali A Shahhararriyar Kasuwar 'Alaba International', Mutane Da Dama Sun Jikkata

An Samu Tashin Hankali A Shahhararriyar Kasuwar 'Alaba International', Mutane Da Dama Sun Jikkata

  • Hankula sun tashi a shahararriyar kasuwar ‘Alaba International’ a ranar Laraba, inda aka kara tsakanin yan kasuwa da bata gari
  • Mutane da dama sun jikkata yayin tarzoman wanda ya wakana a yankin Ojo da ke jihar Lagas
  • Sai dai zuwa yanzu an samu zaman lafiya ya dawo bayan sojoji da yan sanda sun shiga lamarin

Lagos - An samu gagarumin tashin hankali a shahararriyar kasuwar nan ta 'Alaba International’ da ke yankin Ojo ta jihar Lagas a ranar Laraba, 19 ga watan Oktoba.

Jaridar PM News ta rahoto cewa wasu daruruwan bata gari ne suka yi bata-kashi da yan kasuwa a cikin kasuwar.

Yan sanda
An Samu Tashin Hankali A Shahhararriyar Kasuwar 'Alaba International', Mutane Da Dama Sun Jikkata Hoto: Premium Times
Asali: UGC

An tattaro cewa yan kasuwa sun rufe shagunansu yayin da hankalin mutane ya tashi a cikin kasuwar.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Farmaki Wani Gari A Zamfara, Sun Kashe Mutum Daya Da Sace Wasu 8

Bidiyoyi da ke yawo a shafukan intanet sun nuno daruruwan yan daba dauke da muggan makamai kamar su adduna yayin da suka tunkari abokan hamayyarsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An kuma rahoto cewa yan kasuwa da dama da jami’an hukumar tashoshin mota na jihar Lagas sun jikkata a kazamin karon.

Sai da sojoji da jami’an yan sanda kwantar da tarzoma suka shiga lamarin don hana zubar jini tsakanin bangarorin biyu, rahoton Nigerian Tribune.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da dawo da zaman lafiya a kasuwar.

An tattaro cewa shugabannin kasuwar sun yi kokarin fatattakar bata-garin da ke cikin kasuwar ne lokacin da rikicin ya fara.

Wani dan kasuwa mai suna Iheanacho ya fada ma Nigerian Tribune cewa gaba daya abun ya fara ne a ranar Talata lokacin da shugabannin kasuwar suka nemi a fatattaki yan iska daga kasuwar.

Kara karanta wannan

Baba-Ahmed Ya Gargadi Yan Najeriya Akan Su Guje Wa Yan Takara Masu Nuna Kabilanci da Addini a Zaben 2023

Iheanacho ya ce:

“Gaba daya abun ya fara ne a yammacin ranar Talata lokacin da shugabannin kasuwar suka zuba yan doka da wasu yan kasuwa don fatattakar yan iska, da ke sha’aninsu a kasuwar.
“Rikicin ya ci gaba har zuwa safiyar yau lokacin da yan iskan suka raba kansu sannan suka saka mambobinsu a wurare daban-daban na kasuwar don farmakar yan doka da yan kasuwar.”

‘Yan Bindiga Sun Farmaki Wani Gari A Zamfara, Sun Kashe Mutum Daya Da Sace Wasu 8

A wani labarin, 'Yan bindiga dauke da makami sun farmakin garin Hayin Banki da ke karamar hukumar Anka a jihar Zamfara a daren ranar Litnin inda suka kashe mutum daya da kuma awon gaba da wasu takwas.

Majiyoyi daga hedkwatar karamar hukumar sun sanar da Channels TV cewa yan bindigar sun mamayi yankin ne da misalin karfe 11:30 na dare sannan suka fara harbi kan mai uwa da wahabi.

Kara karanta wannan

Abinda Yasa Nake Da Gwarin Guiwar Cewa Ni Zan Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2023, Tinubu Ya Magantu

Mazauna yankin sun ce wasu daga cikin mutanen da aka sace sun kasance ma’aikatan wani kamfanin ruwa da wani manajan gonar kaji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: