Bincike: Gwamnatin Kasar China Ta Bude Ofishin Yan Sanda a Najeriya

Bincike: Gwamnatin Kasar China Ta Bude Ofishin Yan Sanda a Najeriya

  • Wata sabuwar bincike ta bayyana yadda gwamnatin kasar Sin ta bude ofishin yan sanda a Najeriya
  • An ce Kasar Sin na gina ofishsosin ne don hukunta yan kasarta dake aikata kaifuka a kasashen waje
  • Kwanakin baya wani dan kasar Sin ya hallaka har Najeriya da suka soyayya a jihar Kano

Gwamnatin kasar Sin ta bude ofishohin yan sanda a Najeriya da sama da kasashe 20 a fadin duniya don dakile laifukan da yan kasarta ke aikatawa a wadannan kasashe.

Wannan na kunshe cikin rahoton binciken da Safeguard Reporter ya gudanar.

Lesotho, Tanzania da Najeriya ne kasashen Afrika uku da gwamnatin Sin ta gina ofishin yan sanda.

A cewar rahoton:

"Maimakin bada hadin kai da mutunta yancin wadannan kasashe, ta gwammace ta hada kai da wasu kungiyoyi wajen kafa ofishohin yan sanda da kotuna a kasashe masu tasowa wajen hukunta yan kasarta."

Kara karanta wannan

Buhari: Na yi ayyuka masu tasirin da 'yan Najeriya ke alfahari dasu a fadin kasar nan

China
Bincike: Gwamnatin Kasar China Ta Bude Ofishin Yan Sanda a Najeriya Hoto: China
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya cigaba da cewa gwamnatin Sin ta yi ikirarin tsakanin Afrilu 2021 da Yuli 2022, an dawo da sama da yan kasar mutum 230,000 gida don fuskantar hukunci kan laifukan da suka aikata.

Hukumomi a Sin sun bayyana cewa daya daga cikin hanyoyin tilastasu komawa gida shine hana 'yayansu dake Sin zuwa makaranta tare da cin mutuncin yan uwansu, cewar Safeguard.

Ta kara da cewa:

"Yayinda aka kafa wadannan ofishohin don bibiyan yan kasarta da ake yiwa zargin damfara da zambar yanar gizo, China ta haramtawa yan kasarta zuwa wasu kasashe 9 da ake yawan samunsu da wannan laifi."

Najeriya Na Zaman Tsammani Yayinda China Taci Kenya Tara Kan Rashin Biyan Bashi Kan Lokaci

A wani labarin kuwa, Gwamnatin kasar Sin ta bukaci kasar Kenya ta biyar tarar Sh1.312 billion(N4.71 billion) bisa jinkiri wajen biyan kudin bashin da ake binta.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi Ya Yafewa Fursunoni 153, Ya Ba Kowanne N50,000 Kudin Jari

Sin ta baiwa Kenya bashin kudaden ne don gina layin dogon jirgin kasa amma sun gaza samun isasshen kudin shiga don biyan bashin.

Jaridar BusinessDaily Kenya ta ruwaito cewa kasar ta karbi bashin rabin Tiriliyan na Shillings daga wajen Kasar China, don gina layin dogon Mombasa zuwa Naivasha.

A yanzu dai gwamnatin Sin ta hana Najeriya bashin kammala ginin layin dogon Kano-Kaduna- Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida