Wani Gwamna Ya Umurci Dalibai Da Ma’aikatan Gwamnatin Jiharsa Su Fara Sanya Kayan Gargajiya Ranar Juma’a
- An umurci dalibai a makarantun jihar Ondo da su fara sanya kayan gargajiya a ranar Juma’a
- Wannan shine matsayin gwamnatin jihar bayan wata shawara da aka yanke a taron majalisar zartarwa ta jihar
- Bugu da kari, an bukaci ma’aikatan jihar da suma su dunga sanya kayan gargajiya a wannan rana
Ondo – Gwamnatin jihar Ondo karkashin jagorancin Gwamna Rotimi Akeredolu ta umurci dalibai a makarantun kudi da na gwamnati da su koma sa kayan gargajiya duk ranar Jama’a.
Legit.ng ta tattaro cewa wannan shine matsaya da aka cimma yayin wani taro na majalisar zartarwa a ranar Litinin, 17 ga watan Oktoba.
Hakazalika, an bukaci ma’aikatan gwamnati da su dunga sanya kayan gargajiya a ranar Juma’a.
2023: Dan Wani Babban Sarki Da Ya Rasu Ya Fadi Dan Takarar Da Mahaifinsa Ya So Ganin Ya Gaji Buhari
A wani labari na daban, dan marigayi Alaafin, Oba Lamidi Adeyemi 111, Akeem Adeyemi, ya bayyana cewa burin mahaifinsa na karshe shine ganin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban kasar Najeriya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Adeyemi mai wakiltan mazabar AFIJIO/Atiba, Oyo ta gabas, Oyo ta yamma a majalisar tarayya, ya bayyana hakan ne yayin zagayowar ranar haihuwar marigayi basaraken na Oyo a karshen mako, The Nation ta rahoto.
An gudanar da bikin ne a dan karamin filin wasa da ke Ode Aremo, kusa da fadar Alaafin din.
Asali: Legit.ng