Yan Arewa Ni Suke Bukata, Ba Wani Bayarabe Ko Inyamuri ba: Atiku

Yan Arewa Ni Suke Bukata, Ba Wani Bayarabe Ko Inyamuri ba: Atiku

  • Alhaji Atiku Abubakar ya bayyanawa dattawa da matasan Arewa cewa shi suka bukata ba wata kabila ba
  • Wasu Kungiyoyin Arewacin Najeriya sun shirya taron tattaunawa a jihar Najeriya Ranar Asabar
  • Jam'iyyun siyasan Najeriya sun fara gudanar da yakin neman zabensu tun bayan dage takunkumin da INEC tayi

Kaduna - Dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party(PDP), Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa shi yan Arewa ke bukata a 2023 ba dan takara Bayarabe Ko Igbo ba.

Atiku ya bayyana cewa a matsayinsa na dan Arewa, ya shiga kowani lungu da sako na kasar nan kuma ya fahimci ko ina.

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya bayyana hakan ne yayinda yake amsa tambyar Kakakin kungiyar dattawan Arewa, Hakeem Baba-Ahmed a jihar Kaduna ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Yadda Budurwa Ta Kashe Saurayinta Da Wuka Cikin Dare Kusa Da Dakin Hotel

Atiku
Yan Arewa Ni Suke Bukata, Ba Wani Bayarabe Ko Inyamuri ba: Atiku

Kungiyoyin yankin Arewacin Najeriya sun shirya taron tattaunawa da dan takarar a gidan tarihin Arewa House dake jihar Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyoyin sun hada da Arewa Consultative Forum, Arewa House, Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation, Northern Elders Forum, and Arewa Research and Development Project, dss.

Atiku yace:

"Abinda kowani dan Arewa ke bukata shine Dan Arewa kuma wanda ya fahimci kowani sashen kasar nan."
"Dan Arewa bai bukatar dan takara Yoruba ko Igbo, na cikakken dan Najeriya kuma dan Arewa."

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel