Yau Zan Kara Adadin Hadimaina Zuwa 100,000: Gwamna Nyesom Wike

Yau Zan Kara Adadin Hadimaina Zuwa 100,000: Gwamna Nyesom Wike

  • Gwamnan jihar Ribas ya ya bayyana cewa zai kara nadin sabbin hadimansa zuwa dubu dari (100,000)
  • Gwamnan ya bayyana cewa mutane sun ji dadin nadin mutum 50,000 da yayi a farkon makon nan
  • Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP

Jihar Ribas - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya bayyana cewa zai kara adadin nade-naden hadimansa a fannin siyasa daga 50,000 zuwa 100,000.

Wike ya bayyana hakan ne ranar Juma'a, 14 ga Oktoba yayin zaman da yayi da yan jarida a gidan gwamnatin jihar.

Wannan ya biyo bayan cece-kuce da akeyi cewa gwamnan na baiwa mutane mukamai yayinda yake da sauran yan watanni ya sauka daga mulki.

Kara karanta wannan

Idan Na Tona Asirin Ayu, Ko 'Yayansa Sai Sun Guje Masa: Wike

Wiked
Yau Zan Kara Adadin Hadimaina Zuwa 100,000: Gwamna Nyesom Wike

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Wike a farko ya nada mutum 28,000. Daga baya kuma ya kara nadin zuwa 50,0000.

Ya bayyana cewa ya cika dukkan alkawuransa na ayyukan ganin da ido tare da matsawa zuwa gina jama'a a fannin siyasar jihar tasa.

Yace:

"Yau zamu yi zama kuma zamu yi karin zuwa 100,000. Kuma dukkansu yan asalin jihar Rivers ne."
"Babu ruwanku da kudin da za'a biyasu, idan an biyasu ku tambayesu da kanku."
"Hadimai ne na siyasa, ba ma'aikatan gwamnati bane."

Idan Na Tona Asirin Ayu, Ko 'Yayansa Sai Sun Guje Masa: Wike

A wani labarin kuwa, Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya sake tsokano shugaban uwar jam'iyyar PDP, Iyorchia Ayu, kan zargin almundahanar da yayi masa a watan Satumba.

Wike ya kara yanzu da cewa Ayu fa ya karbi milyan dari hannun wani gwamna, sannan ya koma wajen kwamitin gudanarwa ya sake karban wani milyan dari.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: 2023: Sunayen Gwamnonin Kudu 4 Da Aka Tura Su Roki Nyesom Wike

Wike ya bayyana hakan yayin hira da yan jaridar ranar Juma'a a birnin Port Harcourt.

Karo na biyu, Gwamnan jihar Rivers ya hau minbarin fara tonon silili kan wasu jiga-jigan jam'iyyar Peoples's Democratic Party PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida