Muna Shawaran Sake Ciwo Bashi Daga Wajen Asusun Lamunin Duniya, Ministar Kudi
- Gwamnatin tarayya na shawaran ciyo sabon bashin kudin abinci daga wajen asusun lamunin duniya
- Ministar kudi tace za'a ciwo wannan bashi ne saboda asarar amfanin gona da akayi sakamakon ambaliyar ruwan sama a fadin tarayya
- A kasafin kudin 2023 da shugaba Buhari ya gabatar makon da ya gabata, za'a sake cin wani sabon bashin trilliyoyi
Amurka - Ministar Kudi da Kasafin Kudi, Zainab Ahmed Shamsuna, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na shawarar sake ciyo sabon bashi daga wajen asusun lamunin duniya watau IMF.
Zainab ta bayyana hakan yayin taron bankin duniya da IMF da ya gudana ranar Laraba a Washington, babbar birnin Amurka, rahoton TheCable.
Ministar kudin ta kara da cewa ta dade tana tattaunawa da hukumomin kudi don ganin yadda baiwa Najeriya talala wajen biyan kudin basussukan da ake bin kasar.
"Osinbajo Ne Uban Kiristocin Najeriya", Wurinsa Kadai Za Mu Iya Zuwa Ya Share Mana Hawaye, In Ji Rabaran Ali Aba
A cewarta:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Lallai Najeriya ta ci basussuka da yawa cikin shekaru uku zuwa hudu da suka gabata, kuma an yi hakan ne don magance wasu matsaloli da kasar ta fuskanta, duk da cewa ba Najeriya kadai ta fuskanta wadannan matsaloli ba."
"Lokacin karshe da muka karbi bashi wajen IMF shine na SDR na aka baiwa dukkan mambobin (IMF). Yanzu kuma IMF ta fito da sabon bashin abinci da kasashe zasu iya karba."
"Bamu yanke shawara kan haka ba tukun. Sai mu duba sharrudan dake tattare da bashi, domin ganin ko zamu iya saboda bamu son shiga wani shirin IMF."
"Idan zamu iya, zamu yanke shawara kan karban kudi saboda zasu taimaka wajen cika runbunan abinci da magance matsalolin da kasar ke fuskanta."
Zainab tace ambaliyar ruwan saman da aka yi kwanakin nan zai haddasa matsala da hauhawar kayan abinci saboda dimbin asarar amfanin gonan da akayi.
Game da basussukan da ake bin Najeriya yanzu, ministar tace za su yi amfani da kashi 65% na kudin shiga a shekarar 2023 wajen biyan bashi.
Najeriya Na Zaman Tsammani Yayinda China Taci Kenya Tara Kan Rashin Biyan Bashi Kan Lokaci
A wani labarin kuwa, Gwamnatin kasar Sin ta bukaci kasar Kenya ta biyar tarar Sh1.312 billion(N4.71 billion) bisa jinkiri wajen biyan kudin bashin da ake binta.
Sin ta baiwa Kenya bashin kudaden ne don gina layin dogon jirgin kasa amma sun gaza samun isasshen kudin shiga don biyan bashin.
Jaridar BusinessDaily Kenya ta ruwaito cewa kasar ta karbi bashin rabin Tiriliyan na Shillings daga wajen Kasar China, don gina layin dogon Mombasa zuwa Naivasha.
Asali: Legit.ng