Jerin Mutum 11 Dake Dakon Kujerar Gwamnan Borno Zulum A 2023

Jerin Mutum 11 Dake Dakon Kujerar Gwamnan Borno Zulum A 2023

Sama da yan takaran jam'iyyun siyasa guda 11 zasu fafata a zaben gwamnan jihar Borno na shekarar 2023.

Jerin yan takaran na kunshe cikin takardar da hukumar gudanar da zabe ta kasa watau INEC ta saki a Maiduguri.

Shugaban sashen yada labarai da ilmantar da jama'a na INEC a jihar Borno, Malam Shuaibu Ibrahim, ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai NAN ranar Alhamis a Maiduguri.

Ga jerin wadanda zasu fafata a 2023:

 1. Babagana Zulum - All Progressive Congress APC
 2. Ali Jajari - People’s Democratic Party PDP
 3. Babagana Buji - Action Alliance AA
 4. Alhaji Monguno - Action Democratic Party ADP;
 5. Hassan Musa - Allied People’s Movement APM,
 6. Abdulkadir Umar - Action People’s Party APP
 7. Shettima Kakagoni - Boot Party BP
 8. Goni Abdullahi - Labour Party;
 9. Umar Mustapha - National Rescue Movement,
 10. Maigawa Muhammad - People Redemption Party PRP,
 11. Modu Abba - Social Democratic Party SDP,
 12. Fatima Abubakar - African Democratic Congress.

Kara karanta wannan

Atiku, Kwankwaso Ko Obi? APC Ta Fadi Dan Takara 1 Da Zai Fafata da Tinubu, Tace Sauran Cikon Benci Ne

Borno
Jerin Mutum 11 Dake Dakon Kujerar Gwamnan Borno Zulum A 2023

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kayar da Zulum abune mai saukin gaske: Dan takaran gwamnan PDP a Borno

Dan takaran Gwamnan jihar Borno na jam'iyyar PDP, Mohammed Jajari, yace gwamnatin All Progressives Congress (APC) da Gwamna Babagana Umara Zulum a 2023 abune mai sauki gaske.

Jajari yace imani kan hakan yasa ya fito takarar zabe kuma har lashe zaben fidda gwanin jam'iyyarsa.

Yace mutane su daina ganin cewa Zulum yana wani aikin kwarai.saboda a boye babu abinda yake yi face korar ma'aikata da kuntata musu ta hanyar biyansu albashi mara tsoka.

Jajari yace a ranar zabe sai Zulum ya riga rana fadi.

A cewarsa, Zulum bai yi kokarin da ya cancanci a zabeshi ba a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel