Atiku da Okowa Zasu Fitar Da Najeriya Daga Kangin Talauci, Kwamitin Kamfen PDP

Atiku da Okowa Zasu Fitar Da Najeriya Daga Kangin Talauci, Kwamitin Kamfen PDP

  • Tsohon Kakakin uwar jam'iyyar PDP ya yi kira ga yan Najeriya kada su kuskura su sake zaben APC
  • Ologbondiyan yace Atiku ne zai iya fitar da yan Najeriya daga cikin kangin talaucin da suka ciki
  • Hukumar INEC zata gudanar da zaben shugaban kasa ranar 25 ga watan Febrairu, 2023

Abuja - Idan kuka zabi Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa a zaben shugaban kasan 2023 mai zuwa, zasu kawo karshen yunwa, wahala da talaucin da yan Najeriya ke fama da shi, Kakakin kamfen PDP, Mr. Kola Ologbondiyan, ya bayyana.

Ologbondiyan ya bayyana hakan a Abuja yayinda hira da matasan jam'iyyar PDP ranar Talata, rahoton Vanguard.

Ya bayyana cewa idan aka zabi Atiku da Okowa, zasu kawo karshen halin talauci da yan Najeriya ke fama da shi daga raar 29 ga Mayu 2023 da Buhari ya sauka daga mulki.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Kinkimo Manya 3 Domin Su Lallabi Wike Ya Marawa PDP baya

Ologbondiyan
Atiku da Okowa Zasu Fitar Da Najeriya Daga Kangin Talauci, Kwamitin Kamfen PDP
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayi bayanin cewa irin ayarin mutanen da suka tarbi Atiku a Uyo, Akwa Ibom na nuna cewa lallai al'umma na son sa.

A cewarsa:

"Daga cikin yan takara kujerar shugaban kasa, Atiku Abubakar kadai ke da tsarin kawo karshe azaba, yunwa, matsin tattalin arziki, drashin kudi da rashin adalicin da gwamnatin APC ta kawowa yan Najeriya."

Ya yi kira da yan Najeriya kada su zabi wadanda suka kai Najeriya kasa cikin shekaru 7 kacal.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida