Har Yau Idan Na Tuna Abinda Atiku Yayi Lokacin Kashe Deborah Sai Na Yi Kuka, Jarimin Nollywood
- Wani Jarumin finafinai daga Kudancin Najeriya ya bayyana takaicinsa game da abin da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yi
- Jarumin ya bayyana cewa kashe wata ɗaliba mazauniyar jihar Sakkwato da aka yi a watannin baya abin takaici ne
- Sai dai Atiku Abubakar ya bayyana cewa sam ba da izininsa aka saka wancan rubutu da fari ba, hakan ta sa ya sa aka cire bayan suka da Musulmi ƴan Arewa
Wani Jarumin fina-finai Chidi Mokeme ya nuna rashin jin daɗinsa game da yadda tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya goge alhinin da ya yi game da rasuwar wata yarinya a shafukansa na sada zumunta.
Yarinyar mai suna Debora Samuel wacce ke aji biyu a Kwalejin Koyarwa ta Shehu Shagari, ta gamu da fushin wasu matasa ne a jihar Sakkwato bayan zarginta da aikata ɓatance ga shugaban Halitta.
Mokeme ya tabbatar da cewa bai ji daɗin hukuncin da ɗan takarar shugabancin ƙasa a Jam'iyyar PDP ya yi a kan wannan al'amari ba.
Mutane da yawa daga Kudancin kasar nan sun nuna rashin jin daɗinsu musamman a kafar sadarwa ta Twitter tare da sa #JusticeForDeborah (Neman Adalci ga Deborah).
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya goge wannan alhini da ya saka ne a shafinsa na Twitter bayan gamuwa da suka da Alla-wadai da ya sha daga mutanen Arewa.
Sai dai Atiku Abubakar ya bayyana dalilinsa na sa wa a cire wannan rubutu, inda ya bayyana cewa sam babu izininsa aka saka shi tun da fari. Wannan ta sa ya sa aka cire rubutun.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sai dai Mokeme ya nuna baƙin cikinsa game da cewa ɗan siyasar da yake ƙauna sosai ya gaza taya al'ummar Kirista baƙin cikin abin da ya sami Deborah.
"Na ji ba daɗi a lokacin da na hau Twitter na ga cewa Atiku Abubakar ya goge rubutunsa na taya alhini da ya yi. Sai na shiga mamakin wato shi ko tausayin wannan yarinya bai ji ba kenan?" Ya faɗa idanunsa cike da ƙwalla.
"A duk san da na tuna, nakan ji kamar na zubar da hawaye game da wannan abin baƙin cikin," a cewar Mokeme.
Kalli bidiyon:
Ban yi Zaɓen Tumun Dare Ba Wajen Zaɓar Okowa a kan Wike – Atiku
Atiku Abubakar Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP mai adawa yace bai yi zaɓen tumin dareba a zabar dan takarar mataimakinsa Mista Ifeanyi Okowa.
Ya bayyana hakan ne bayan karramarwa da shugaban kasa yai masa da lambar yabo ta (CON), a cikin wani takaicacceyar wallafa da ya yi a shafinsa na Tuwita, inda ya taya gwamnan jihar Delta murnar samun lambar girman.
Asali: Legit.ng