An Kama Wani Uba da Ɗansa da Laifin Zambar Naira Biliyan 5.6

An Kama Wani Uba da Ɗansa da Laifin Zambar Naira Biliyan 5.6

  • A ranar biyu ga watan Agustan shekarar nan, aka gurfanar da wani ɗa da uba da zargin zamba cikin aminci
  • Sai dai waɗanda ake zarga sun musanta zargin da ake yi musu kan amfani da kuɗi har Naira biliyan biyar wajen gudanar da harkokin banki ba a bisa ƙa'ida ba
  • Don haka kotu ta saka ranar sake duba yiwuwar ba da beli waɗanda ake zarga da kuma fara sauraren shari'arsu

Hukumar Hana Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zangon Ƙasa, EFCC, ta yi nasarar kama wani uba da ɗansa a bisa zargin yin zamba cikin aminci na Naira biliyan biyar da dubu ɗari shida.

Mutane biyun dai sun gurfanar ne a gaban wata babbar kotu da jihar Legas inda waɗanda ake tuhuma, Daniel Jayeoba da kuma mahaifinsa Emmanuel Jayeoba da kanfaninsu mai Wales Kingdom Capital Limited a ranar 2 ga watan Agusta, 2022 a gaban mai Shari'a Nicholas Oweibo.

Kara karanta wannan

Abun Tausayi: An Gano Wani Bawan Allah Tsirara da Aka Kulle Tsawon Shekara 20 a Kaduna

Ana tuhumarsu ne game da yin ayyukan kasuwanci na banki ba tare da samun lasisi ba a dokance, inda kuma suka musanta wannan zargi tare da samun beli, rahoton TheNation.

EFCC Lagos
An Kama Wani Uba da Ɗansa da Laifin Zambar Naira Biliyan 5.6 Hoto: EFCC
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tuhumar da ake musu dai ta yi daidai da wata saɗara ƙunshe cikin dokokin tasarifin kuɗi da na zargin yin sama da faɗi da Naira biliyan biyar da miliyan shida da dubu ɗari biyu da ɗari shida da tamanin da biyar.

Cikin lafuzan na kotu ya ƙunshi;

"Adewale Daniel Jayeoba da Emmanuel Adewunmi Jayeoba, a tsakanin shekarun 2019 da 2020, a wannan jiha ta Legas, kun haɗa baki a tsakaninku tare wajen yin amfani da kuɗi har Naira biliyan biyar da miliyan shida da dubu ɗari biyu da ɗari shida da tamanin da biyar wajen gudanar da ayyukan banki ba tare da samun amincewar hukumomi ba.

Kara karanta wannan

Shin Ko Kun San Babu Buƙatar Cire Dattin Kunne Kwata-kwata?

Wannan dai ya saɓa wa sashen na 18(a) na ta'ammali da kuɗi na shekarar 2012 wanda kuma ke tattare da hukunci kunshe cikin sashe na 15(3) na wanann kundi na laifuka."

Tuni lauya mai ƙara, Chinenye Okezie, ya roƙi kotun da ta saka ranar sauraren shari'ar, yana mai fatan za a tsare su a gidan yari.

Amma lauyen mai kare masu ƙara, I.A Raji ya sanar wa da kotun cewa, kotu ta bayar da belin waɗanda ake zargi, sai dai ba su iya kai wa ga cika sharuɗan belin ba.

Raji ya yi roƙi kotun da ta saka ranar mafi kusa domin sake duba sharuɗan belin.

Mai Shari'a, Aneke, ya ɗage shari'ar har zuwa 17 ga watan Oktoba, 2022 da kuma 6 ga watan Disambar, 2022 domin sauraren koken mai neman beli da kuma yin shari'a tare da umarnin iza ƙeyar waɗanda ake tuhuma zuwa gidan yari

Asali: Legit.ng

Online view pixel