Kasafin Kuɗi 2023: N22.44Bn Gwamnati ta Ware Wa ƴan Gidan Kaso
- A satin da ya gabata ne dai Shugaba Buhar ya mika kasafin kuɗin gaban haɗakar majalissar ƙasa
- Kasafin wanda ya kai kimanin Naira Tiriliyan 20 da ɗoriya ya zarce na shekarun baya da akayi
- Kudin da aka ware don ciyar da kula da yan gidajen yari ya kusa bilyan ashirin da uku
Gwamnatin tarayya ta yi hasashen kashe sama da Naira biliyan 22 wajen samar da kayan abinci ga hukumar da ke Kula da Gidajen Gyaran Hali a shekarar 2023.
Abinda ake hasashen za su kashe a jimlace ya tasar ma N22,447,582,237, rahoton Vanguard.
Wannan adadin dai wani ɓangare ne na kudirin gwamnatin tarayya a daftarin kasafin kudin shekarar 2023, baya ga ware wa Ma'aikatar Cikin gida zunzurutun kudi Naira biliyan 304.39.
A cikin wannan adadi da aka ware, Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida an sanya mata nata hasashen abinda zata kashe gaba ɗaya kuma ana sa ran ya tasar ma Naira biliyan 2.66, yayin da Hukumar Kula da Gidajen Gyara Hali ake sa ran zasu kashe Naira biliyan 91.79.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sauran da kasafin kuɗin nasu ke alaƙa da Ma'aikatar Gida sun haɗa da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa da a ke sa ran zata kashe Naira biliyan 76.51, da kuma Jami'an Tsaron Farin Kaya ta Civil Defense suma nasu ya tasar ma Naira biliyan 117.15. kuma Hukumar kashe Gobara ta ƙasa ake sa ran zata samu Naira biliyan 15.74.
A jimlace dai; Hukumomin Kashe Gobara, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa da Hukumar Kula Da Gidajen Gyaran Hali Ta kasa zasu kashe kimanin Naira miliyan 522.59.
Ginin manyan gidajen yari masu daukar mutane 3,000 a jihohin Osun, Plateau, Gombe da Abia wanda ake ci gaba da yi zai lakume sama da Naira biliyan 1.55.
Har ila yau, ana ci gaba da gina wasu cibiyoyi makamanta masu ɗaukar mutane 3,000 a Kano, da Abuja, da Bori, da Damaturu da kuma kara dakunan kwana a wasu wuraren wanda ake sa ran zai ci Naira miliyan 783.3.
Game da na’urar tantancewa ta gidan yari, alburusai da makamai da sauran kayan aikin tsaro, ana sa ran zasu laƙume sama da Naira biliyan 1.44.
Kasafin Kudi: Buhari Ya Fadawa Majalisa Ba Zai Cigaba da Biyan Tallafin Fetur a 2023 ba
Shugaba Muhammadu Buhari ya koka a kan yadda ake batar da makudan biliyoyin kudi a wajen biyan tallafin man fetur a Najeriya.
Yayin da yake gabatar da kasafin kudin shekarar 2023, Daily Trust ta rahoto Muhammadu Buhari ya na wannan kuka da ya je gaban majalisa.
Ganin halin da kasar take ciki a halin yanzu, Shugaban Najeriyan yace ba zai yiwu a cigaba da batar da makudan kudi a kan tallafin man fetur ba.
Asali: Legit.ng