Ana Bikin Duniya: Yadda Ƴan Sanda Suka Gano Gawarwaki a Ofishin shugaban Asibiti

Ana Bikin Duniya: Yadda Ƴan Sanda Suka Gano Gawarwaki a Ofishin shugaban Asibiti

  • Rundunar ƴan sanda ta kama wani tsohon babban daraktan kula da lafiya (CMD) na babban asibitin Kaiama da ke jihar Kwara
  • A cewar ƴan Sandan "Dakta Adio Adeyemi Adebowale", na da alaƙa da mutuwar wasu mata biyu da ba'a gan su ba tun daga shekarar 2021
  • A yayin wani bincike da aka ba da izini, jami'an tsaro sun gano gawarwakin matan da aka binne a ofishin sa

Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta ce ta gano gawar wata mata da aka bayyana bata a watan Nuwamban 2021 a cikin ofishin babban likitan asibitin Kaiama da ke karamar hukumar Kaiama ta jihar kwara.

Wani rahoto da BBC Pidgin ta fitar ya ce rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa an gano hakan ne a yayin gudanar da bincike kan Dokta Adio Adeyemi Adebowale da ake zargin yana da alaƙa da wani kisan kai a jihar Edo.

Kara karanta wannan

Lokacin Da Na Hau Mulki Kukan Tashin Bama-Bamai Yan Najeriya Ke Yi, Buhari

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Ajayi Okasanmi, lamarin na da nasaba da ƙarar da ƙorafe-ƙorafe da aka shigar kan ɓatan Nofisat Halidu, da aka ce ta bace a asibitin tun a karshen shekarar 2021.

SP Okasanmi ya kara da cewa bisa ga umarnin kwamishinan ‘yan sandan, Paul Odama, an fara gudanar da bincike wanda ya bawa jami’an sa tabbatar da cewa matar da ta bata budurwar Adebowale ce.

Kaiaima
Ana Bikin Duniya: Yadda Ƴan Sanda Suka Gano Gawarwaki a Ofishin shugaban Asibiti
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gawa Biyu aka Samu a Ofishinsa.

Kamar yadda sanarwar Okasanmi ta bayyana, jami’an sun tilasta bude kofar ofishin Adebowale inda suka gano ruɓɓarɓiyar gawar wata mata da aka binne a wani kabari da aka yi da tiles.

Sanarwar ta kara da cewa

"Wani daga cikin jami'an mu yaga alamar kamar an taba tayil din ofishin, da ga dukkan alamu an yi sabo kuma ya banbanta da na jiki. Haka yasa muka duba, ai kuwa sai g gawar wata mata a cikin wajen."

Kara karanta wannan

An damke Soja yana baiwa masu garkuwa da mutane hayar bindiga AK-47

Bayan dogon bincike a ofishin sai ga wata gawar "bayan mun ci gaba da bincika ofishin, sai ga wani abun zubda shara, ko da muka duba sai gawar Nofisat wadda aka kawo rahotan ta bata.

Rundunar tace ta samu ƙarin wasu abubuwa a ofishin wanda ake zargin, wanda suka haɗa da ɗan kamfe, wayoyin hannu da kuma mayafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida