Ni Ba Ɓarawo Bane: Shugaban PDP ya magantu kan zargin badaƙalar kuɗi

Ni Ba Ɓarawo Bane: Shugaban PDP ya magantu kan zargin badaƙalar kuɗi

  • Ko a cikin satin nan ma dai kwamitin amintattun jam'iyar yayi zama kan wannan lamarin
  • Ana zargin dai batan kuɗi kimanin N122.4 a tsakanin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar
  • Ayu wanda ke maida martani kan zarginsa da ake, ya ce zargin ba shi da tushe balle makama, a matsayina na dan Adam ina da nakasu, amma sata ko wawashe dukiyar al’umma ba ta ciki in ji Ayu.

Ya yi magana a kan zargin da ake yi na cewa alawus-alawus na gidaje da aka biya mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar, wani ƙulle-ƙulle ne da sharri kawai.

A cewarsa, ya karbi ragamar shugabancin jam’iyyar ne domin dawo da martabar ta da kuma mayar da ita ofis. Yana mai cewa jam'iyyar PDP ba an yi ta ne domin ta taka rawar adawa ba, sai don ta ci zabe da samar da shugabanci mai ma’ana ga ƴan kasa.

Kara karanta wannan

Allah Ya Wadarar A Sake Baiwa PDP Amanar Baitul Malin Al'umma, Lai Mohammed

Ayu ya bayyana haka ne a lokacin da yake maraba da kungiyar zababbun mambobin jam’iyyar da suka kai masa ziyarar goyan baya a hedikwatar Jam'iyyar PDP ta kasa, a ranar Juma’a nan.

Ayu, wanda kuma ya bayyana cewa ya umurci Sashen Kudi da kula da sabunta asusun jam'iyar da kashe kudi, su gabatar da bayani ga kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa (NEC) a bikin cika shekara da rantsar da ƴan kwamitin.

Yace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Wataƙila kuna karanta abubuwa da yawa kuma kuna tsammanin martani na. Ba koyaushe muke magana ba, saboda muna son ci gaba da gina haɗin kai a cikin jam’iyyar. Ba ma son rigima a cikin ƴaƴan jam'iyyar PDP. Idanuwanmu na kan babban hoto cin zaben 2023.”
“Saboda haka, kada mu bari hankalin mu ya bar kar tsarin mu da ƙa'idojin mu. In kun yi la'akari rikici ne yasa na zama shugaba, dan haka dole mu magance shi"

Kara karanta wannan

Obi Ɗan-Gata: Gwamnoni 18 Ne Ke Marawa Obi Baya, Ohanaeze

“Babban kwamitin gudanarwa (NWC) sun tattauna kan batun Bayar da Gidaje. An dai amince gaba daya cewa babu wani cin hanci ko wani nau'insa da aka yi. Tuni dai suka fitar da bayyanai kan hakan, shi yasa kuka ga komai ya lafa”

Tun da farko a nasa jawabin, shugaban kungiyar, Hon. Yunana Iliya, ya ce mambobin sun je sakatariyar jam’iyyar ne domin nuna goyon bayansu ga shugaban jam’iyyar na kasa, tare da yin alkawarin biyayya ga jam’iyyar da babban kwamitin gudanarwa (NWC) wanda Ayu ke jagoranta.

Ya kara da cewa,

"Muna goyon bayan kuri'ar amincewar da babban kwamitim gudanarwa (NEC) ya ba ku, kuma muna kira ga duk ƴan jam'iyyar amanna kuma su kudirci aikin ceton PDP," in ji shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida