Allah Ya Sitiri Buƙwui A Sake Bawa PDP Amanar Lalitar Gwamnati
- Lai Mohammed ya bukaci a gudanar da bincike a kan jam’iyyar PDP da shugabanninta na kasa
- Yana bayyana hakan kan naira miliyan 122.4 da wasu shugabannin jam’iyyar suka mayar asusu
- Ministan ya ce halin da jam’iyyar PDP ke ciki a halin yanzu ya nuna Ƙarara cewa har yanzu ba su ɗau wani darasi ba.
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ya yi wa babbar jam’iyyar adawa ta PDP kaca-kaca, in da ya bayyana jam’iyyar PDP a matsayin jam’iyyar da ke da ɗabi’ar wawashe dukiyar Nijeriya.
Lai yace PDP zata ci gaba da hakan muddin aka bata dama a zaben 2023 mai zuwa, rahato jaridar TheCable.
Legit.ng ta tattaro cewa ministan ya yi wa jam’iyyar adawar martani ne kan lamarin da ya janyo cece-kuce, inda wasu mambobin kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP na kasa suka mayar da zunzurutun kudi har Naira miliyan 122.4 da aka tura musu.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai a birnin Arusha na kasar Tanzaniya, inda ake ci gaba da gudanar da taron hukumar kula da yawon bude ido ta duniya karo na 65, Lai Mohammed ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Idan mutum zai yi sata akaran kansa, to mai zai hana ace yayi in ya samu ta jama’a”
"Matsalar ita ce PDP ba za ta taba canzawa ba, kuma kamar yadda masu magana ke cewa ne, damisa ki sabo."
Ministan ya yi tanbihi kan faduwarsu zaben 2015, wanda yace ya kamata ace sun yi karatun ta nutsu, amma dukkan alamu sun nuna jam’iiyar bata shiryu ba.
Yace
“Allah Ya kiyaye, idan sun sake samun lalitar gwamnati, to ina tabbatar ma baza su bar ko kobo ba. Munsan abinda muka tarar da muka karbi mulki a 2015 har yanzu muna jin radadin abun”
"Muna fata 'yan Najeriya yanzu sun ga yadda jami’iyyar PDP take badaƙala, da kuma yadda zasu yi in suka danka musu mulki"
Lai Mohammed ya yi kira da a binciki babban kwamitin ayyuka na kasa kan badaƙalar kudade.
A halin da ake ciki, ministan ya ce akwai bukatar a binciki jam’iyyar PDP dan su bada ba’asi kan yadda suka samu wannan kuɗaɗen da kuma yadda akai badakalarsa.
Ya bayyana cewa jam’iyyar sa ta APC ba ta taɓa biyan kudi zuwa asusun yan kwamitin ayyuka na jam’iyar ba.
Mohammed ya ce:
"A iya tunani na ban taba ganin inda aka ce an sa mana kudi wai da sunan kudin gida ko zirga-zirga a asusun mu ba tun da ga jam’iyyar ACN har zuwa APC."
Atiku ya bayyana Lai Muhammad a matsayin maƙaryaci.
A wani martani da ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi, ya ce ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed ya shiga tarkon yin ƙarya ne.
Ka Yi Kokari: Matashi Ya Zana Katafaren Hoton Peter Obi Jikin Bango A Jihar Kaduna, Yan Najeriya Sun Yi Martani
Atiku ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga ikirarin Mohammed na cewa ya kwaikwayi tsarin tattalin arzikin shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC a kundin yakin neman zabensa.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa jam’iyyar APC da shugaba Buhari ba su da wani shiri na mulki ko da takarda ɗaya ba da za a kwatanta da cewa itace tasawirar tattalin arziki ko makamancin haka.
Asali: Legit.ng