Bayan Shafe Watanni Uku, DPOn Yan Sanda Ya Shaƙi Iskar Yanci

Bayan Shafe Watanni Uku, DPOn Yan Sanda Ya Shaƙi Iskar Yanci

  • Garkuwa da Mutane dai dan karbar ƙudin fansa na ƙara ta'azzara a yankunan arewa masu yamma na Nijeriya
  • Ko a farkon Shekarar nan ma dai sai da masu garkuwa da mutane suka sace tare da kashe wasu daga cikin fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa kaduna
  • Jami'an tsaron Nijeriya na ta bayyanawa al'umma ƙasar ƙoƙarinsu na ganin an shawo kan matsalar

Kaduna - An sako babban DPOn ‘yan sanda na shiyyar Birnin Gwari a jihar Kaduna, Sani Mohammed Gyadi-Gyadi watanni uku bayan da aka yi garkuwa da shi.

Sakin na sa na zuwa ne kwana guda bayan da aka sako sauran fasinjojin jirgin ƙasan kaduna Zuwa Abuja guda 23 da aka yi garkuwa da su a ranar Laraba nan data gabata.

Hakan ya biyo bayan wani Aikin ƙazo na haɗin gwuiwa da sauran jami'an tsaro suka yi in ji rahoton da jaridar PRNigeria ta fitar.

Kara karanta wannan

Sojinmu Gwaraza ne, Babu Aikin da Ba Zasu Iya ba: Buhari Yana Murnar Dawowar Fasinjojin Jirgin Kasa

An dai garzaya da Gyadi-gyadi zuwa wata cibiyar lafiya a jihar Kaduna dan duba lafiyarsa.

“Yana cikin kwanciyar hankali, amma likitoci suna lura da yanayin lafiyarsa,” inji wani na kusa da baturen ƴan sandan kaman yadda ya shaida wa jaridar PRNigeria.

Gyadi-Gyadi
Bayan Shafe Watanni Uku, DPOn Yan Sanda Ya Shaƙi Iskar Yanci Hoto: @SaharaReporters
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wata majiya da ba ta so a bayyana ta ba ta shaidawa jaridar PRNigeria cewa "ƴan kammala duk wani yunkuri ne a labarar data gabata dan ganin an kwato jami'in.

Majiyar ta ƙara da cewa "Duk da cewa ba zan so in faɗi abun da zamu yi ba, amma zanso sanar da ku cewa zamu ƙubutar da jami'in"

Tun da fari dai iyalan ɗan sandan sun roki gwamnatin Najeriya da ta taimaka wajen ganin an sako shi daga hannun Masu garkuwa da mutanen.

A cikin watan Yuni ne aka yi garkuwa da Gyadi-Gyadi a kan hanyar sa ta zuwa Birnin Gwari a lokacin da yake ƙokarin karbar aiki a matsayin Baturen Ƴan sandan shiyyar.

Kara karanta wannan

Jami’an Kwastom Sun Kama Bindigu, Harsasai, Buhun Shinkafa 7000 Da Jarkokin Mai

PRNigeria ta tattaro cewa ‘yan ta’addan da suka sace shi tun farko sun bukaci iyalansa da su biya kuɗin fansa naira miliyan 250 kafin su rage zuwa Naira miliyan 80.

Ƴan uwa da abokan arziki dai sun tara kuɗin tare da damkawa Ƴan ta'adar amma daga ƙarshe basu sake shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida