Fasto Ya Sauya Rayuwar Yar Gidan Magajiyar Ya Tsinta A Titi A Legas

Fasto Ya Sauya Rayuwar Yar Gidan Magajiyar Ya Tsinta A Titi A Legas

  • Labari ne mai cike da ban mamaki da sosa zuciya wata mai zaman kanta wadda ake kira da lizzy ta samu sauyin rayuwa bayan haduwarta da wani malamin majami’a
  • Rayuwar Lizzy ta canja ne daga yanke kauna zuwa rahama, sabida yadda take da zuciya mai kyau
  • Limamin ya maida rayuwar Lizzy zuwa ta abin kwatance daga wacce take da abar kyama

Akwai darussa da yawa a rayuwa wanda wani lokacin zaka ga canji, wani lokacin kunci ko akasin haka.

Amma kadai hakan na faruwa ne ga wanda suke da hankalin da nutsuwar ganewa.

Labari ne dangane da yadda rayuwa ta canjawa wata mai zaman kanta bayan haduwarta da wani malamin majami’a.

All Lizy
Fasto Ya Auri Yar Gidan Magajiyar Da Ya Sauya Rayuwarta Bayan Tsintarta A Titi Hoto: African History Archive
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Shekaruna 40, Babu Mashinshini Balle In Haihu, Budurwa Ta Koka a Bidiyo

Matashiyar mai suna Lizzy, wacce take da tana mu’amala da kayan shaye-shaye da kuma take zaman kanta, amma al’amura sun fara canjawa Lizzy ranar da ta hadu da wani malami coci, wanda aka fi sani da Fasto Tony Rapu, wanda ke wa’azi ya nuna sha’awar tarayya da ita.

Abu daya kara wa abun armashi shine yadda hotunan lizzy yake ada kafin ta canza da kuma bayan haduwarta da wannan malamin cocin.

Da take magana a lokacin da suka fara haduwa, Lizzy ta ce ba ta ji dadi ba lokacin da Fasto Tony ya zo wajenta, saboda ta saba yin mu’amala da wanda ba malamai ba sai gama gari kawai.

Fasto Tony wanda ya sauya rayuwar lizzy ya kasance lauya, marubuci, kuma marubuci.

Labarin Lizzy ya ja hankalin mutane da dama a kafafen sada zumunta ciki harda;-

Norma Tayawa-Guimas:

"Allah ya canza mana idan mun yardazai iya”

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa CBN Zata Sauya Wasu Takardun Kudaden Najeriya

Hazekiah Aba:

"A'a dama ire-iren su ya kamata ace suna aura."

Oladeji Olakunle:

"Ba gashi ba da sukai auren faston ya canja mata rayuwa."

Moremoney Luka Jonathan:

"A'a ba fa iya fasto ne ya kamata yayi haka ba muma ya kamata mu gwada

Anselen Chineke:

"wai da gaske idona ne suke kallon wannan canjin rayuwar."

Olanrewaju Ahmed Sanusi:

"mutane ne ke bawa kansu shawarar yadda zasu canja."

Yawanci dai a birane yan mata masu zaman kansu na fitowa rike da kayan maye tsaye a layi suna jiran masu tayi.

Kamar yadda yake a bayyane da kuma yadda muatne ke maganar ire-iren bidiyon da ake tashe a kafafen sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida