Hotunan Sauran Fasinjoji 23 na Jirgin Kasan Abj-Kd da Suka yi Kwana 192 Hannun ‘Yan Ta’adda
- Kwamitin fadar shugaban kasa na ceto sauran fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya sanar da kubutar fasinjojin
- Kamar yadda Yusuf Usman ya bayyana, wurin karfe hudu na ranar Laraba aka ceto fasinjojin da suka yi kwana 191 a daji
- A hotunan jigatattun jama’ar da aka gani, an gansu a mota kirar bas wacce aka kwaso su a cikinta
Dukkan fasinjojin farmakin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna na ranar 28 ga watan Maris 2023 sun shaki iskar ‘yanci kamar yadda gwamnatin tarayya ta bayyana.
Farfesa Usman Yusuf, sakataren kwamitin shugaban ma’aikatan tsaro ya sanar da hakan a ranar Laraba.
“Ina farin cikin sanar da kasar nan da duniya cewa wurin karfe 4 na yammacin ranar Laraba, 5 ga watan Oktoban 2022. Kwamitin shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Leo Irabor ya karbo tare da ceto sauran fasinjoji 23 dake hannun mayakan Boko Haram a farmakin ranar 28 ga watan Oktoban 2022.”
- Yace.
Ga wasu daga cikin hotunan mutum 23 da aka saki ranar Laraba bayan kwashe wata shida a hannun ‘yan ta’addan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da Duminsa: ‘Yan Ta’adda Sun Sako Sauran Fasinjoji 23 na Harin Jirgin Kasan Abj-Kd
A wani labari na daban, ‘yan ta’adda da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun sako ragowar fasinjoji 23 da suka yi garkuwa da su.
Sakataren kwamitin shugaban ma’aikatan tsaro, Usman Yusuf ne ya tabbatar da hakan kamar yadda Channels Tv ta rahoto.
Yusuf yace an sako fasinjojin da suka kwashe watanni shida hannun miyagun ‘yan bindigan a ranar Laraba wurin karfe 4 na yamma.
Asali: Legit.ng