Kara Tsawo Nake Duk Bayan Wata 3 Ko 4: Wani Dogon Mutum Ya Ba Da Tarihinsa A Wani Bidiyo

Kara Tsawo Nake Duk Bayan Wata 3 Ko 4: Wani Dogon Mutum Ya Ba Da Tarihinsa A Wani Bidiyo

  • Sulemana Abdul Samed ya shahara a duniyar yanar gizo saboda yanayin halittar da Allah yayi masa, ya kasance dogon mutum
  • Mutumin wanda aka fi sani da Awuche a garinsa ya ce lamarin ya fara ne a cikin shekarar 2015
  • A yanzu haka, mai son angwancewar yace a wannan al’amari nasa, yakan kara tsawo bayan watanni uku ko hudu

Wani mutumi mai suna Sulemana Abdul Samed wanda aka fi sani da Awuche da ake yiwa kallon mutum mafi tsawo a kasar Ghana ya bayyana cewa yana kara tsawo duk bayan watanni uku ko hudu.

Abdul ya yi fice a duniyar yanar gizo kuma ya zama shahararre a garinsa saboda yanayin halitarsa ta dogon mutum.

Sulemana
Kara Tsawo Nake Duk Bayan Wata 3 Ko 4: Wani Dogon Mutum Ya Ba Da Tarihinsa A Wani Bidiyo Hoto: @bbcnewspidgin
Asali: Instagram

Abun ya fara ne a 2015

A wata hira da BBC News Pidgin, mutumin yace ya fara lura da ya fara tsawo ne a cikin shekarar 2015.

Kara karanta wannan

Dan Achaba Ya Baje Kolin Dankareren Gidan Da Ya Ginawa Mai Shirin Zama Amaryarsa, Hoton Ya Ja Hankali

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abdul wanda tsawonsa ya kai sahu 9 da inci 6 ya ce wata rana haka sai ya lura harshensa ya kara fadi kuma yana shan wahala wajen jan numfashi.

“Na wayi gari wata rana sai na lura cewa harshena ya kara fadi a bakina har ta kai bana iya numfashi.”

Ya nuna jin dadinsa kan yadda tsawonsa ke janyo hankalin mutane gareshi a wajen taruka, yana mai cewa yana farin ciki da yadda Allah ya halicce shi.

A cewarsa, sai da ya nemi mai gyaran takalmi ya gwada shi domin yi masa takalmi na musamman da zai dace da shi.

Abdul ya kara da cewar an fada masa abun da ke damunsa sunansa ‘gigantism’ wanda ke sa yara ko manya yin tsawo fiye da kima. Ya kuma ce yana fatan yin aure wata rana harma ya samu ‘ya’ya.

Kara karanta wannan

Wani Dan Wasa a Najeriya Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Ya Mutu Ana Tsaka da Buga Kwallo

Jama’a sun yi martani

@sy_via_lyn ya ce:

“Yace yana kara tsawo har yanzu wannan babban abu ne fa kada ya zo ya fi gida tsawo fa.”

@jenoko4real ya ce:

“Ya je Amurka ya zama mai buga wasan kwallon raga. Murmushinsa na

@sznnn_x tace:

“Mutumin nan na bukatar kulawar likita sosai. Kuma yana bukatar ayi masa tiyata cikin gaggawa kamar yadda likitansa ya bayar da shawara. Ina masa fatan alkhairi.”

Ka Fi Mai Hannu: Matashin Da Bai Da Hannaye Ya Ba Da Mamaki Yayin da Yake Tuka Mota Kamar Kwararren Direba

A wani labarin, wani mutumin kasar Kenya mai suna Sammy Bravo ya burge mutane da dama a soshiyal midiya saboda tarin baiwar da Allah yayi masa.

Abun da yasa labarinsa ya bayar da mamaki shine ganin cewa an haife shi ba tare da hannaye ba, amma kuma yana iya yin abubuwa da dama da masu hannu ke yi.

Kara karanta wannan

Wani Gwamnan APC Ya Yi Magana Kan Bidiyon Tinubu Da Ake Yaɗa Wa a Kafafen Sada Zumunta

An gano Sammy, wanda ke karfafawa mutane gwiwa da zantuka yana ayyuka ba tare da taimakon wani ba ciki harda tuka mota.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng