Dan Achaba Ya Baje Kolin Dankareren Gidan Da Ya Ginawa Mai Shirin Zama Amaryarsa, Hoton Ya Ja Hankali

Dan Achaba Ya Baje Kolin Dankareren Gidan Da Ya Ginawa Mai Shirin Zama Amaryarsa, Hoton Ya Ja Hankali

  • Wani hazikin dan achaba ya nuna cewa mutum na iya cimma abubuwa da dama a rayuwa a kowani irin bangare na kasuwancinsa
  • Mutumin mai suna Kahii Ga Cucu ya wallafa hoton wani hadadden gida da ya ginawa kansa da wacce za ta zama abokiyar rayuwarsa a gaba
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun bayyana ra’ayoyinsu game da lamarin inda wasu da dama suka yaba tsaruwar gidan

Wani dan achaba mai suna Kahii Ga Cucu ya burge jama’a a soshiyal midiya bayan ya nuna wani dankareren gida da ya kerawa kansa.

Da ya je wani shafin Facebook mai suna Dream House and Building Forum don wallafa hoton gidan nasa, mutumin ya nuna farin cikin mallakar gida sukutum duk da irin fadi tashin da yake yi wajen samun na kai.

Dan Achaba da gida
Dan Achaba Ya Baje Kolin Dankareren Gidan Da Ya Ginawa Mai Shirin Zama Amaryarsa, Hoton Ya Ja Hankali Hoto: Kahii Ga Cucu
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa gidan nasa ne shi da wacce za ta zama matarsa a gaba sannan ya tunatar da jama’a cewa kowani irin kasuwanci yana da amfani. Mutumin kasar Kenyan ya rubuta:

Kara karanta wannan

Lambar Girma: Yadda Ake ta Surutu Yayin da Manyan Na-kusa da Buhari Suka Tashi da Matsayi

“Duk da kasancewana dan achaba, na yi nasarar mallakawa kaina da mai shirin zama matata a nan gaba wannan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"#KowaniFadiTashiYanaDaAmfani.”

Wallafar tasa na dauke da martani fiye da 3k da kuma ‘likes’ 59k inda jama’a suka taya shi murnar wannan babban nasara da ya samu.

Jama’a sun yi martani

Eunice Nkilasi ya ce:

“Na tayaka murna dan uwa, kuma ina addu’ar wannan ya zama mafarin alkhairi, Allah ya yi maka babban tanadi a gaba, kuma Allah ya albarkace ka da samun mace tagari mai tsoron Allah, na tayaka murna ina maka fatan alkhairi.”

Lawrence Kamau Nganga ya ce:

“Dan Allah kada kace duk da kasancewarka…Kowani fadi tashi yana da amfani, kana iya kasancewa manaja ko dan kabu kabu, abun da yafi shine ka zama mai lissafi. Idan bah aka ba na tayaka murna dan uwa! Ka yi kokari.”

Kara karanta wannan

Idan Na Siya Dankareriyar Mota Kada Kuyi Mamaki, Budurwa ‘Yar Najeriya Da Ke Sana’ar Jari Bola

Mercy Kirwa ta ce:

“Ya yi kyau, Allah yasa ka ci moriyar aikin hannunka, mafarki da addu’o’I su ke zama nasararn rayuwa, Allah ya albarkaceka, na tayaka murna…”

Shekaru 3 Bayan Mutuwarsa: An Binne Mutumin Da Ya Auri Mata 20 Da Haihuwar Yara Fiye Da 100

A wani labarin kuma, mun ji cewa bayan shekaru uku da mutuwarsa, an binne wani mutumin kasar Ghana mai suna Mista Wilson Gbli Nartey daga garin Ningo a yankin Accra.

Ya mutu ne a watan Satumban 2019. An tattaro cewa mutumin mai shekaru 103 a duniya yana da matan aure 20 sannan yana da yara 111 da jikoki fiye da 500.

Babban abun da zai ba mutum mamaki shine yadda majiyoyi suka bayyana cewa Mista Wilson Gbli Nartey ya kula da dukka mata da yaran nasa a lokacin da yake raye. Kuma ya kasance mutum mai kima da mutunci.

Kara karanta wannan

Kana Da Kyau: Budurwa ‘Yar Najeriya Ta Tunkari Wani Saurayi A Cikin Banki, Ta Karbi Lambar Wayarsa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng