Maigadin Coci Ya Yi Murabus Daga Aiki, Sannan Ya Koma Ya Sace Kudin Sadaka N600,000
- Jami'an yan sanda masu sintiri sun damke maigadin coci makare da kudade a jihar Ekiti
- An bayyana matashi tare da gungun masu garkuwa da mutane gaban yan jarida a ranar Talata
- Matashin yayi bayanin cewa ya yi aiki a coci kafin yayi murabus kuma ya san sirrin cocin
Ekiti - Hukumar yan sandan a jihar Ekiti sun damke wani matashi mai suna Olufemi Akindele kan laifin satan kudin sadakan Coci N620,115 a jihar Osun.
Akindele ya sace kudin ne a cocin Christian Apostolic Church a Ikeji Arakeji
Akindele na cikin mutum 20 da hukumar yan sandan jihar Ekiti ta kaddamar a ranar Talata, 4 ga watan Oktoba, 2022 a Ado Ekiti, rahoton Punch.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, Sunday Abutu, ya ce sun damke Akindele ne kan babur hanyar Igara Odo da jaka cike da kudade barkatai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yace:
"Yayin bincike, ya bayyana cewa tun daga Ekiti ya tafi sansanin cocin CAC dake Ikeji jihar Osun don sace kudin sadaka daga asusun coci N620,115."
Kakakin yan sandan yace barawon ya bayyanawa manema labarai cewa shi tsohon mai gadi ne a cocin, kuma sannin tsirrin waje ya sa ya tafi zuwa satan kudin.
Katsina: 'Yan Bindiga Sun Kama Barawo, Sun Mika Shi Hannun Jami'an Tsaro
A wani abu da yayi kama da kura ke kiran kare maye, wata kungiyar 'yan bindiga sun cafke wani barawo a jihar Katsina.
PRNigeria ta tattaro cewa, barawon ya kware wurin cire rodi da karafuna daga kangon gine-gine a kauyukan jihar.
Barawon 'dan jari bolan ya shiga hannun 'yan bindigan dake sintiri a baburansu kamar yadda aka tattaro.
Asali: Legit.ng