Da Dumi-dumi: Wani Gwamna A Najeriya Ya Sanar Da Yiwa Ma’aikatan Jaharsa Karin Albashi
- Gwamna Sanwo-Olu na Lagas ya bayar da umurnin yiwa gaba daya ma'aikatan gwamnati a jihar karin albashi
- Gwamnan ya ce wannan umurnin ya kasance ne saboda matsi da tsadar rayuwa da ake fama da shi a kasar nan
- Sanwo-Olu ya bayar ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 4 ga watan Oktoba, yayin da yake jawabi ga ma'aikatansa
Lagos - Gwamnan jihar Lagas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana cewa gwamnatinsa na kokarin yiwa ma’aikatan gwamnati karin albashi, jaridar The Cable ta rahoto.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin biyan duk bashin kudaden fansho da ma’aikata ke bi a karshen watan Oktoba, Vanguard ta rahoto.
Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 4 ga watan Oktoba, yayin da yake jawabi ga ma’aikata a sakatariyar jihar da ke Alausa, Ikeja.
Ka Yi Kokari: Matashi Ya Zana Katafaren Hoton Peter Obi Jikin Bango A Jihar Kaduna, Yan Najeriya Sun Yi Martani
Gwamnan ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Na duba koina kuma na san cewa akwai matsi a kasar. Na san cewa, a kasar akwai hauhawan farashin kayayyaki.
“A zaman majalisarmu, na umurci ofishin shugaban ma’aikata da ma’aikatar ma’aikata, horarwa da fansho da su fara aiki kan yadda za mu yiwa gaba daya ma’aikatanmu karin albashi.”
“Za mu iya aikata wannan. Lagas ce kan gaba yayin da saura ke bin sahunta a Najeriya. Wajen Karin albashi, muna kan gaba kuma.
“Za mu yi amfani da taken nan na ‘Buga’ wajen biyan albashi. Ba za mu jira Karin mafi karancin albashin gwamnatin tarayya ba.
“Mun fara bin tsarin. Ina mai tabbatar maku cewa zuwa farkon shekara mai zuwa za a fara aiwatar da shi.
“Bama son jiran kungiyoyion ma’aikata su rike mu kafin mu yi abun da ya kamata.”
Idan Na Siya Dankareriyar Mota Kada Kuyi Mamaki, Budurwa ‘Yar Najeriya Da Ke Sana’ar Jari Bola
A wani labarin, wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta wallafa wani bidiyo da ke kunshe da yadda take gudanar da sana'arta na jari bola a watan Satumba.
Ta bayyana cewa kada mutane su yi mamaki idan ta tara kudin siyan mota kirar Marcedes Benz daga wannan sana’a tata.
Budurwar ta nuna raunukan da ta ji sakamakon tattara kayan jari bola daga wurare daban daban tana sanya su a cikin buhuhuna.
Asali: Legit.ng