Tinubu Na Nan Lafiya Lau A Landan, In Ji Kakakin Kamfen APC

Tinubu Na Nan Lafiya Lau A Landan, In Ji Kakakin Kamfen APC

  • Wani hadimin Tinubu ya tabbatarwa da al’umma cewa maigidansa yana nan cikin ƙoshin lafiya
  • Bayo Onanuga ya bayyana cewa hotunan da ake yaɗawa ƙarya ne na Tinubu duk na bogi ne
  • Kuma Ya bayyana dalilan da ya sa Tinubu bai samu halartar tarun yarjejeniyar zaman lafiya da aka ƙulla a tsakanin ƴan takara

Abuja - A cewar daraktan kafafen sada zumunta da yaɗa labarai na Takarar Shugabancin Ƙasa na jam’iyyar APC, Bayo Onanuga, Tinubu lafiyarsa ƙalau.

Onanuga ya bayyana hakan ne biyo bayan shaci-faɗi da ake yi game da rashin ganin ɗan takarar shugabancin ƙasar a yayin gudanar da wata jarjejeniya ta zaman lafiya da aka yi a Abuja a tsakanin masu neman takarar shugabancin ƙasa a Najeriya, inda ake cewa rashin lafiya ce ta hana Tinubun halarta.

Kara karanta wannan

2023: Na Sadaukar da Rayuwata da Komai Ga Al'ummar Jihar Katsina, Ɗan Takarar APC Dikko

Onanuga
Tinubu Na Nan Lafiya Lau A Landan, In Ji Kakakin Kamfen APC Hoto: APC
Asali: UGC

A yayin da yake ƙaryata wannan zargi game da wasu hotuna da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta, a shafin Fesbuk a jiya, Onanuga ya tabbatar da cewa Tinubu yana nan cikin ƙoshin lafiya a London, rahoton TheNation.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Bari na tabbatar wa da masu san sanin gaskiyar inda Tinubu yake kan cewa yana gidansa da ke ƙasar Ingila a garin Landan,” a cewar Onanuga.

“Don haka, ina mai tabbatar muku da cewa, duk hotunan nan da ke yawo a soshiyal midiya na ƙarya ne. Tinubu Na Nan Lafiya Lau"

Sannan ya cigaba da cewa, ɗan takarar ya bar ƙasar nan ne domin yin wani taƙaitaccen hutu, domin shirya wa shirin yaƙin neman zaɓensa da ake shirin farawa.

Tinubu Ya Naɗa Aisha Buhari Shugabar Tawagar Kamfen Mata

A wani labarin kuwa, Jam’iyya mai mulki a Nijeriya ta APC, ta sanar da nada Matar shugaban kasa Aisha Buhari a matsayin wadda zata jagoranci mata a kamfen din jami’iyyar na 2023, a yau asabar.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito Yayin da Ake Jita-Jitar Wani Gwamnan PDP Ya Jingine Atiku, Ya Goyi Bayan Obi a 2023

Sauran wadanda zasu taka rawa a tawagar sun hada da Sanata Oluremi Tinubu, Sanata mai wakiltan Legas ta tsakiya a zauren majalisar dattawa a wa'adi na uku a majalisar dattawa kuma tsohuwar uwargidan tsohon gwamnan jihar Legas, Nana Shettima, tsohuwar uwargidan gwamnan jihar Borno kuma uwargidan dan takarar mataimakin shugaban kasa jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags: