Shugaba Buhari Zai Yi Jawabi ga yan Najeriya Misalin Karfe 7 Gobe Da Safe

Shugaba Buhari Zai Yi Jawabi ga yan Najeriya Misalin Karfe 7 Gobe Da Safe

  • Shugaban Muhammadu Buhari zai yi jawabin murnar ranar yancin kai na karshe a matsayinsa na shugaban Najeriya
  • Najeriya ta samu yancin kai ranar 1 ga Oktoba 1960 daga hannun turawan mulkin mallaka
  • Najeriya ta cika shekaru 62 da samun yancin kai amma har yanzu kasar bata shiga sawun kasashen da suka cigaba ba

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabi na musamman ga yan Najeriya da safiyar Asabar, 1 ga watan Oktoba 2022, fadar shugaban kasa ta bayyana haka.

A jawabin da Bashir Ahmad, hadimin shugaban Buhari ya saki ranar Juma'a a Facebook, ya bayyana cewa Buhari zai yi wannan jawabi ne don murnar zagayowar ranar yancin kan Najeriya.

A cewarsa, za'a haska jawabin misalin karfe 7 na safe.

"Shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga kasa gobe, 1 ga Oktoba, 2022, da karfe 7 na safe, cikin shirye-shiryen murnar cikar Najeriya shekaru 62 da samun yancin kai.#NigeriaAt62

Kara karanta wannan

Hotunan Motar Kudin Banki Da Ta Kama Da Wuta Tsakiyar Titi A Kebbi

BUhari
Shugaba Buhari Zai Yi Jawabi ga yan Najeriya Misalin Karfe 7 Gobe Da Safe
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel