Hukuncin Kotu: Ba Zamu Koma Aji Ba, Kungiyar ASUU Ta Daukaka Kara
- Malaman jami'a sun ce ba zasu yarda ba, sun daukaka kara babbar kotun Afil ta tarayya bisa shari'ar kotun ma'aikatan Najeriya NIC
- Gwamnatin tarayya ta shigar da kungiyar ASUU kotu bisa yajin aikin da ta shiga tun watan Febrairu
- Watanni bakwai kenan daliban jami'o'in jiha da na tarayya a fadin kasar na zaman gida
Abuja - Kungiyar Malaman jami'o'in Najeriya ASUU ta daukaka kara kotun Afil dake zamanta a birnin tarayya Abuja ranar Juma'a, 23 ga Satumba.
Malaman sun bukaci kotun ta soke hukuncin da kotun ma'aikata NIC tayi na cewa su janye daga yajin aikin watanni bakwai da suke ciki, rahoton Vanguard.
Kungiyar, ta hannun lauyanta, Femi Falana SAN, ta gindayo lamura 14 da akayi kuskure a shari'ar farko.
FG Zata Janye Rijistar Kungiyar ASUU, Ta Bayyana Dalilinta
Alamu sun bayyana a ranar Laraba cewa gwamnatin tarayya na iya janye rijistar kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, a matsayin kungiyar kwadago sakamakon gazawarta na gabatar da rahotonta na tantancewa kamar yadda doka ta tanada a shekaru biyar da suka gabata.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tuni dai aka bayyana cewa, magatakardar kungiyar kwadagon ya rubutawa kungiyar takardar tuhuma kan dalilin da ya sa ba za a janye satifiket din rijistar ta ba saboda taka doka.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da malaman jami’o’i a fannin likitanci suka nemi ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta Najeriya da ta yi musu rijista a matsayin kungiyar kwadago ta daban a karkashin kungiyar Nigerian Association of Medical and Dental Academics, NAMDA.
Asali: Legit.ng