Karon Farko, Jakadan Kasar China Ya Yi Magana Kan Kwace Kadarorin Najeriya Idan Ta Gaza Biyan Bashi
- A karon farko, gwamnatin kasar Sin ta yi tsokaci kan abinda zai faru idan Najeriya ta gaza biyan basussukan da ake binta
- Gwamnatin kasar Sin ta baiwa Najeriya basussukan gina layin dogon jirgin kasa da wasu gine-gine
- Shugaba Buhari ya bukaci shugabannin kasashen duniya su taimaka wajen yafewa Najeriya bashi
Abuja - Jakadan kasar Sin zuwa Najeriya, Mr Cui Jianchun, ya bayyana cewa gwamnatin kasarsa ba ta da niyyar kwace kadarorin Najeriya idan ta gaza biya basussukan da ake binta.
Jianchun ya bayyana hakan ranar Alhamis yayin ziyarar da wakilin Sin kan lamuran Afrika, Liu Yuxi, ya kaiwa karamin Ministan harkokin wajen Najeriya, Zubairu Dada, a Abuja.
Sun kai masa wannan ziyara ne don karfafa alakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Sin, rahoton NewTelegraph.
Ya ce kasar Sin ta yarda da Najeriya kuma ba ta da niyyar kwace kadarorin Najeriya inda aka ki biyan bashin da aka karba don gine-gine.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa, kwace kadarori bai cikin yarjejeniyar da aka yi tsakanin kasashen biyu.
Yuxi ya godewa Najeriya bisa yanke alaka da kasar Taiwan kuma ya yi alkawarin ko kada kasar Sin ba zata amince da katsalandan cikin lamuran wasu kasashe ba.
Ku Taimaka Ku Yafe Mana Basussukan Da Ake Binmu: Shugaba Buhari Ya Roki Shugabannin Duniya
A jiya, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira da shugabannin kasashen duniya su yafewa Najeriya da kasashe masu tasowa basussukan da suke binsu saboda halin matsin tattalin arzikin da suke ciki.
A jawabin da yayi a taron gangamin majalisar dinkin duniya ranar Laraba, Buhari yace kasashe masu tasowa na fuskantar kalubale da dama, cike har da rashin iya bisa basussuka.
Ya bukaci shugabannin duniya su taimaka su sanya baki.
Asali: Legit.ng