Gobe Juma'a Zan Tona Asirin Wasu Shugabannin Jam'iyyar PDP, Nyesom Wike
- Rikicin da ya 'dai'daita 'yayan jam'iyyar adawa ta PDP ya ki ci, ya ki cinyewa ana saura mako guda fara kamfe
- Gwamna Nyesom Wike yayi alkawarin tona asirin wasu jiga-jigan jam'iyyar a gobe Juma'ar nan
- Gwamnan na jihar Rivers tare da wasu gwamnoni sun tsame kansu daga yakin neman zaben Atiku
PortHarcourt - Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya lashi takobin tona asirin wasu shugabannin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) masu ikirarin su iyayen jam'iyyar ne.
Wike yace gobe Juma'a zai gabatar da hirar tona musu asiri, rahoton TheNation.
Yace idan yayi hakan ya sauke nauyi da hakkin da ke kansa saboda haka duk dan Najeriyan da ya ga daman cigaba da girmamasu sai ya cigaba.
Wike ya ce ta wani dalili wadanda suka gaza hada kan 'yayan jam'iyyar zasu iya hada kan yan Najeriya.
2023: Gwamnan PDP Mai Karfin Fada A Ji Ya Bayyana Matsayin Jam'iyyar Janyewar Wike Da Mutanensa Daga Takarar Atiku
Gwamnan ya bayyana hakan ranar Alhamis yayin zama da masu ruwa da tsakin jam'iyyar PDP na jihar Rivers.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar PDP Ta Kira Zaman Gaggawa Bisa Ballewar Mabiya Wike
Uwar Jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP a ranar Laraba ta kira zaman gaggawa bisa baran-baran da wasu jiga-jiganta sukayi da yakin neman zaben jam'iyyar.
Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, da wasu jiga-jigan jam'iyyar sun sanar da cewa babu ruwansu da yakin neman zaben Atiku.
Sun lashi takobin cewa muddin Iyorchia Ayu zai cigaba da zama kan kujerar shugaba, babu ruwansu da jam'iyyar.
Sakamakon haka, shugabannin jam'iyyar sun shiga gannawar sirri don tattaunawa kan illar da hakan zai yiwa shirye-shiryen yakin neman zaben 2023.
Asali: Legit.ng