Hukumar EFCC Ta Magantu Kan Dalilinta Na Kai Samame Gidan Alkali Mbaba Da Ke Kano
- Hukumar EFCC ta bayyana cewa bata kowani bincike kan Jusutis Ita Mbaba, alkalin kotun daukaka kara, reshen Kano
- A cikin wata sanarwa da ta saki, hukumar ta yi watsi da rahotannin cewa jami’anta sun mamaye gidan alkalin
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawarar ta ce jami’anta sun ziyarci wani gidan Justis Mbaba amma tace batun ya shafi mai gidan ne ba wai alkalin ba
Kano - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta yi watsi da rahotannin cewa jami’anta sun kai mamaya gidan alkalin kotun daukaka kara, reshen Kano, Justis Ita Mbaba.
EFCC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, 21 ya watan Satumba ta hannun kakakinta, Wilson Uwujaren.
Ta ce sabanin rahotanni, jami’anta sun ziyarci gidan Mbaba da ke unguwar Sheikh Yusuf Adam Game, hanyar Race Cross Road, yankin Nasarawa, jihar Kano domin tantance gidan.
Ya kara da cewa duk da cewar jami’an hukumar sun ziyarci gidan Mbaba, alkalin kotun daukaka karar baya karkashin bincike.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jawabin ya ce:
“An janyo hankalin hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, zuwa ga wasu rahotanni da ke yawo a soshiyal midiya, da ke zargin cewa jami’anta, reshen Kano sun mamayi gidan alkalin kotun daukaka kara, reshen Kano, Justis Ita Mbaba, da ke unguwar Sheikh Yusuf Adam Game, hanyar Race Cross Road, yankin Nasarawa, Kano.
“Gaskiya ne cewa jami’an hukumar sun ziyarci gidan na Hon. Justis Mbaba, a wani shiri na tantance ginin, sakamakon wani lamari da ya shafi mai gidan, babu gaskiya a batun alakanta alkalin kotun daukaka karar da wani bincike. Bayanai sun nuna cewa Mai shari'a Mbaba ba shine mai wannan gida ba kuma don haka baya cikin kowani bincike da hukumar ke yi.
“Muna fatan jadadda cewa Hon. Justis Ita Mbaba baya karkashin kowani bincike na EFCC. Hukumar na ganin mutuncin bangaren shari’a kuma ba za ta taba yin wani abu don cin zarafin kowani jami’in kotu ba.”
Dole a Binciki Sule Lamido da ‘Ya ‘yansa Kan Zargin Satar Naira Miliyan 712 inji Kotu
A wani labari na daban, Babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja ta yanke hukunci cewa dole Sule Lamido da wadanda ake tuhuma su amsa zargin da ake yi masu.
Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa ta wallafa labarin yadda ta kaya a zaman kotu a ranar Litinin a shafinta a Facebook.
A jiya Alkalin kotun tarayya, Ijeoma Ojukwu tayi watsi da rokon da Lauyan Sule Lamido yake yi a zargin da ake yi masu na satar kudi, Naira miliyan 712.
Asali: Legit.ng