Na Bannatar Da Kudi N8m Wajen Shan Kwaya: Matashin Da Ya Tuba Ya Baiwa Matasa Shawara
- Wani matashi ya yi bayanin yadda ya tsira daga ta'amuni da kwaya bayan shekara da shekaru
- A hirar da aka yi da shi, ya bayyana yadda ya kusa sayar da gida daya tilo da ya mallaka don sayan kwaya
- Ya baiwa Matasa shawara su guji kwaya saboda ba alkhairi bane garesu ko kadan a rayuwa
Wani matashi masanin ilmin zamani na Komfuta, Nelson Oriyomi, ya bayyana yadda Allah ya tsirartar da shi daga ta'amuni da kwaya bayan tsawon shekaru.
A hirarsa da jaridar Punch, matashin ya yi bayanin yadda ya bannatar da kudi milyan takwas da ya tara wajen shan kwaya.
Matashin a kwanakin baya ya bukaci mutane a kafar sada ra'ayi da sada zumunta su taya shi murnar tsira daga harkar kwaya.
Yadda ya fara
Nelson yace tun a baya yana shan Wiwi amma wani abokinsa ya bashi shawaran ya fara shan wani abu mai suna 'Meth'.
Yace:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Shekaru hudu da suka gabata, wani abokina ya fada min zai bani wani abu wanda idan na sha zan ji dadi da kuzari."
Sai da ya kusa sayar da gidansa don siyan kwaya
Nelson ya yi bayanin yadda ya kashe dukkan kudaden da ke asusun bankinsa milyan takwas wajn shan kwaya kuma har ya kusa sayar da gidansa.
A cewarsa, kwayar na da tsadar tsiya kuma ko dadewa ba tayi a jikin mutum.
Yace:
"Kwaya na da tsada saboda gram daya N6,000. Na rasa dukkan kudina, na sayar da dukkan abubuwan da na mallaka, har da wayata. Har na kusa sayar da gidana kuma sa'an da nayi shine takardun gidan na hannun mahaifiyata kuma ta ki bani."
"Kafin shiga harkar kwaya, na tara N8m amma na rasa komai."
Yadda na daina sha
Nelson ya bayyana cewa sai da ya gudu daga Najeriya ya koma Ghana don nisanta daga dukkan abokansa masu shaye-shaye na tsawon watanni bakwai.
Na Ga Al'arshin Ubangiji: In Ji Bokan Da Ya Farka Daga Akwatin Gawa Kwana Biyu Bayan Mutuwarsa A Nasarawa
Yace da farko ya daina shan 'Meth' saboda ko kudin saya bai da shi. Daga baya kuma ya daina shan Wiwin.
A cewarsa, yana da diya mace daya kuma ya fahimci abinda yake yi zai cutar da diyarsa.
Yace:
"Kwaya na lalata rayuwa, dukiya, rana gobe da manufofi. Mutum zai rasa hanyoyin nasara a rayuwa."
Asali: Legit.ng