Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Justice Ariwoola Matsayin Alkalin Alkalan Najeriya

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Justice Ariwoola Matsayin Alkalin Alkalan Najeriya

  • Bayan watanni biyu, majalisar dokokin tarayya ta amince da bukatar Buhari na nadin sabon Alkalin Alkalai
  • Majalisar ta tafi hutun dogon zango na makonni shida kuma tun lokacin basu zauna don tabbatar da shi ba
  • Alkali Olukayode Ariwoola ya gaji Alkalin Tano Muhammad wanda yayi murabus a watan Yuni

Abuja - Majalisar dattawan tarayya ta amince da nadin Justice Olukayode Ariwoola matsayin sabon Alkalin Alkalan Najeriya (CJN).

Tabbatar da Justice Olukayode Ariwoola ya biyo bayan amincewa da mafi akasarin yan majalisar sukayi a ranar Laraba, 21 ga watan Satumba, 2022.

Yayin zaman tabbatar da shi, Alkalin ya amsa tambayoyi da dama da Sanatocin suka yi masa.

Sanatocin da suka yi masa tambayoyi sun hada da mataimakin shugaban majalisa, Sanata Ovie Omo-Agege, Sanata Opeyemi Bamidele, Sanata Philip Aduda, Sanata Gabriel Suswan da Sanata Bala ibn Na Allah.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Mukaddashin Alkalin Alkalan Najeriya

Ariwoola
Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Justice Ariwoola Matsayin Alkalin Alkalan Najeriya Hoto: Presidency
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

TheNation ta ruwaito cewa misalin karfe 12:45, Sanatacon suka bukaci Alkalin ya tafi bayan amsa dukkan tambayoyin da akayi masa.

Bayan haka, Shugaban majalisar, Ahmad Lawan, ya tambayi Sanatocin shin a amince da shi matsayin Alkalin Alkalai? Sai suka amince.

Majalisar dattawa zata binciki Alkalin Alkalai da yayi murabus, Tanko Mohammad, bisa zargin rashawa

A Yuni, Majalisar dattawar Najeriya ta bayyana cewa zata gudanar da sabon bincike kan tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, CJN Tanko Mohammad bisa zargin rashawa da sauran Alkalan kotun ke masa.

Kwamitin harkokin shari’a ta majalisar ta bayyana hakan a ranar Talata, 28 ga watan Yuni, 2022, rah rahoton Punch.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, ya umurci kwamitin dake karkashin Sanata Opeyemi Bamidele, su binciki zargin da ake yiwa tsohon Alkalin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel