Sarki Ya Gargaɗi FG: Kada Ku Kai Matasan Najeriya Bango, Ku Kawo Karshen Yajin ASUU
- Babban Sarkin yarbawa, Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, ya gargaɗi gwamnatin tarayya game da yajin aikin ASUU
- Basaraken ya bukaci FG ta gaggauta magance yajin aikin don dakile ɓarnar da matasa ka iya yi idan aka kai su wuya
- Har yanzu dai ɗalibai na zaune a gida sakamakon yajim aikin kungiyar ASUU tun watan Fabrairu
Ooni na masarautar Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi (Ojaja na III) ya gargaɗi gwamnatin tarayya da Malaman jami'o'i ka da su kuskura su kai matasa bango ta hanyar gaza kawo ƙarshen yajin aikin ASUU.
Sarkin ya yi wannan gargaɗin ne yayin hira da 'yan jarida jim kaɗan kafin fara shagulgulan kwana Bakwai a wani ɓangaren murnar zagayowar Al'adar Olojo a Ile-ife.
Yace ya zama dole gwamnati, cikin lamari na gaggawa, ta shawo kan yajin aikin ASUU domin daƙile haɗarin fusatar matasan Najeriya, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar sarakunan gargajiya a Najeriya (NCTRN) yace zai amfani da wannan lokacin na keɓewa da bauta wajen neman taimakon Allah ya warware matsalolin da suka addabi Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da ƙasar ke shirye-shirye tunkarar babban zaɓe a shekara mai zuwa, Basaraken ya ce:
"Matasa sun fusata kuma babu wanda zai ce musu don me suke fushi, ka duba tsawon watannin da suka kwashe a zaune a gida. ASUU da FG su haɗa kansu su kawo karshen yajin aikin nan."
"Saboda ba zamu iya dakatar da fusatar matasa ba idan suka fita hayyacinsu. Sun fara tsohe manyan Tituna kuma suna barazanar garƙame filayen jirgin sama, hakan alama ce ta cewa an kai su maƙura."
"Shekarata Bakwai kenan a kan karagar Sarauta ina wa al'umma aiki da maida hankali na musamman kan matasa, na jaraba matasa a manyan ayyuka na kuma sun nuna zasu iya. Don haka ina kira ga gwamnati ta duba wannan sashin ta yi gyaran da ya dace."
Ɗalibai sun toshe hanyar jirgin sama a Legas
A wani labarin kuma Daliban Sun Fito Zanga-Zanga, Sun Tare Hanyar Filin Jirgin Saman Legas Saboda Yajin Aikin ASUU
Wani bidiyo ya nuna lokacin da matasa suka mamaye wani titin jihar Legas domin nuna dawa da yajin aikin ASUU.
Matasan suna ta rera wakokin neman gwamnati ta waiwayi ASUU, kana ASUU din ma ta duba bukatar dalibai.
Asali: Legit.ng