NDLEA Ta Bankado Babban Dakin Ajiye Hodar Iblis, Ta Kwace Mai Darajar Biliyan N193bn

NDLEA Ta Bankado Babban Dakin Ajiye Hodar Iblis, Ta Kwace Mai Darajar Biliyan N193bn

  • Hukumar NDLEA ta kai samame wani rumbun ajiye miyagun kwayoyi a jihar Lagas inda tayi ram da hodar iblis masu yawan gaske
  • Nauyin hodar iblis da aka kama ya kai tan 1.8 yayin da darajarsa ya kai dala 278, 250,000 wanda yayi daidai da biliyan N194, 775,000,000
  • Jami’an hukumar sun kuma cika hannu da mutane hudu da kuma wani dan kasar Jamaica da manajan dakin ajiyan

Lagas - Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, sun farmaki wani babban dakin ajiya a yankin Ikorodu da ke jihar Lagas inda aka kama hodar iblis da ya kai nauyin tan 1.8 (kilo 1,855).

Darajar wannan hodar iblis da aka kama a dakin ajiyar ya kai $278, 250,000 wanda yayi daidai da biliyan N194, 775,000,000, jaridar PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Mahaifiyar Tsohon Shugaban EFCC, Ibrahim Magu, Ya rasa Mahaifiyarsa

Akalla masu fataucin miyagun kwayoyi hudu ciki harda dan kasar Jamaica da manajan dakin ajiyan aka kama a shiryeyen harin wanda ya shafe tsawon kwanaki biyu a wurare daban-daban a jihar Lagas.

Masu fataucin kwayoyi
NDLEA Ta Bankado Babban Dakin Ajiye Hodar Iblis, Ta Kwace Mai Darajar Biliyan N193bn Hoto: @pmnewsnigeria
Asali: Twitter

Mutanen da aka kama sun hada Soji Jibril, mai shekaru 69 dan Ibadan jihar Oyo; Emmanuel Chukwu, mai shekaru 65 daga Ekwulobia, jihar Anambra; Wasiu Akinade, mai shekaru 53 daga Ibadan, jihar Oyo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sune Sunday Oguntelure, mai shekaru 53, daga Okitipupa, jihar Ondo da kuma Kelvin Smith, mai shekaru 42, dan asalin Kingston, Jamaica.

Dukkaninsu mambobin kungiyar hada-hadar miyagun kwayoyi da hukumar ke bibiya tun a shekarar 2018.

An farmaki rumbun wanda ke a gida mai lamba 6 Olukuola crescent, Solebo estate, Ikorodu, a ranar Lahadi, 18 ga watan Satumba.

An kuma kama masu harkar a masauki da mabuyarsu da ke wurare daban-daban na Lagas tsakanin daren Lahadi da safiyar Litinin, 19 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Nasara Daga Allah: An Kama Wani Kasurgumin Ɗan Bindiga da Sojan Bogi a Jihar Zamfara

Binciken farko ya nuna cewa an ajiye miyagun kwayoyin ne a dakin daga inda kungiyar ke kokarin sayar da su ga masu saye a Turai, Asiya, da sauran sassan duniya.

An zuba kwayoyin a cikin manyan jakunkunan matafiya guda 10 da kuma randuna 13.

Femi Babafemi, daraktan labarai na hukumar NDLEA ya tabbatar da lamarin ga jaridar PM News.

NDLEA Tayi Ram da Mai Tsohon Ciki Dauke da Miyagun Kwayoyi

A wani labarin, hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta damke wata mata mai tsohon ciki mai shekaru 25 dauke da kwayoyin methamphetamine a garin Auchi dake jihar Edo.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a Abuja ranar Lahadi.

Babafemi yace wacce ake zargin mai suna Haruna Favour, wacce aka kama ranar Juma'a, an kama ta dauke da nau'ikan wiwi da magungunan ruwa masu dauke da codeine.

Kara karanta wannan

Elizabeth II: Za a Kashe Kusan Naira Biliyan 4 Wajen Bikin Jana’izar Sarauniyar Ingila

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng