Majalisar Wakilai Za Ta Dawo Zama A Ranar 20 Ga Watan Satumba A Zauren Wucin Gadi
- Majalisar wakilai za ta dawo zamanta a ranar 20 ga watan Satumba bayan hutun shekara da ta tafi tsawon watanni biyu
- A wannan karon, majalisar za ta dawo zama ne a zauren wucin gadi sakamakon gyara da ake yi a tsohon zauren nata
- Saboda rashin sarari a wannan zaure na wucin gadi, hadiman yan majalisa ba za su samu wajen zama ba
Majalisar wakilai ta kasa za ta dawo zama a ranar 20 ga watan Satumba a zaure na wucin gadi.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Yahaya Danzaria, magatakardar majalisa a ranar Lahadi, 18 ga watan Satumba a Abuja, jaridar Premium Times ta rahoto.
Mista Danzaria ya ce sakamakon gyare-gyaren da ke gudana a tsohon zauren majalisar, ana sanya ran Mmbobin za su dawo zama a sabon zauren da aka tanada da kujerar zaman mutum 118 kacal.
Ya ce an fadada sabon zauren ta hanyar samar da wani bene wanda zai dauki kujeru 236, yana mai cewa an hada dakunan da na’urar murya da kuma manya-manyan abun kallo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kuma, ya ce babu kebabbun kujeru baya ga wanda aka tanada ga shugaba da manyan jami’ai, yana mai cewa duk sauran kujeru zai kasance ne daidai da zuwan mutum, jaridar The Guardian.
Ya ce:
“Yana da matukar muhimmanci a sani cewa saboda wannan tsari na wucin gadi ne, babu wani tanadi da aka yiwa hadiman yan majalisa saboda rashin sarari.”
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rahoto cewa a ranar 20 ga watan Yuli, majalisar ta tafi hutun shekara na watanni biyu gabannin zangon karshe na majalisa ta tara.
Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, a ranar 14 ga watan Satumba ya yi kira ga a gaggauta gyare-gyaren da ke gudana a zauren majalisar gabannin cikar wa’adin Agusta 2023 da aka bayar.
Gbajabiamila ya duba muhimman bangarori na aikin, musamman zauren majalisar wakilai, waje da kuma mashigin ginin.
Jerin Sunayen Yan Siyasar Najeriya Da Suka Mallaki Fitattun Jaridu Da Tashoshin Talbijin
A wani labari na daban, mun ji cewa a Najeriya da sassa da dama na duniya, siyasa da aikin jarida na tafiya ne kafada da kafada, inda mutane daga wadannan bangarori ke gwabzawa yayin da wasu ke cin moriyar dukkanin bangarorin biyu a lokaci daya.
Wasu manyan yan siyasar Najeriya sun mallaki wasu manyan kafofin watsa labarai, inda a wasu gabar yake kasancewa rade-radi.
Sai dai kuma a wannan shafin, Legit.ng ta binciko zahirin gaskiya inda ta tattaro jerin wasu manyan yan siyasa a kasar wadanda suka zuba jari sannan suke kama kudi a bangaren jarida.
Asali: Legit.ng