Ambaliyar Ruwa Ta Tashi Al'ummar Garuruwa Sama da 10 a Jihar Jigawa
- Matsanancin ruwan sama da ya haddasa Ambaliya ya tashi mutane a ƙauyuka aƙalla 11 a ƙaramar hukumar Ringim, jihar Jigawa
- Shugaban ƙaramar hukumar, Shehu Sule Udi, yace ruwan ya lakume rayukan mutane, gwamnati na iya kokarinta
- Ya nemi gwamnatin jiha, tarayya da masu hannu da shuni su taimaka wa mutanen da suka rasa komai nasu sakamakon ibtila'in
Jigawa - Labarin da muka samu daga jihar Jigawa a arewa maso yammacin Najeriya ya nuna cewa aƙalla ƙauyuka 11 ruwa ya lalata a ƙaramar hukumar Ringim.
Shugaban ƙaramar hukumar, Honorabul Shehu Sule Udi, shi ya faɗi haka yayin wata hira da manema labarai a sasanin 'yan gudun Hijira da ke garin Ringim.
Yace matsanancin ruwan ya barnata yankunan kana ya tilasata wa mutanen da ke zaune a ciki yin ƙaura daga gidajensu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban ƙaramar hukumar ya yi bayanin cewa mutane da dama sun rasa rayukansu, ɗaruruwan gidaje sun nutse, gonaki sun lalace da sauran dukiyoyin da aka yi asara duk sakamakon Ambaliya daga Dam ɗin Tiga, jihar Kano.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wane garuruwa lamarin ya shafa?
A jawabinsa, Sule Udi, yace garuruwan da lamarin ambaliyar ya tasa sun haɗa da Dabi, Majiyawa, Dingare, Gabarin, Yandutse, Malamawar Yandutse, Cori, Gujaba, Sankara, Auramo da Garin Gada.
Ya ƙara da cewa gwamnatin ƙaramar hukumar ta kwashe mutanen da jarabawar ta shafa zuwa sansanin yan gudun hijira dake Ringim da Gerawa, kuma tana kokarin sama musu abinci, ruwan sha da magunguna.
Bugu da ƙari, Ciyaman ɗin ya yi roko ga gwamnatin jiha, FG da ɗai-ɗaikun mutane musamman masu hannu da shuni, su taimaka wa waɗannan bayin Allah da Allah ya jarabta cikin gaggawa.
Malam Ibrahim, ɗaya daga mutane da ruwa ya raba da mahallansu a ƙauyen Majiyawa, yace Ruwan ya yi awon gaba da gidajensu da dukkan kayayyakin da suka mallaka da ya haɗa da abinci da tufafi.
Legit.ng Hausa ta rahoto cewa aƙalla mutum Takwas aka tabbatar sun gamu da ajalinsu, wasu biyar suka jikkata sakamakon haɗarin kwale-kwale a Ringim makon da ya shuɗe.
A wani labarin kuma kun ji cewa Adadin Mutanen da Suka Mutu a Ambaliyar Ruwan Jigawa Ya Karu Zuwa 51
Al'umma na cigaba da aikin tsamo gawarwaki biyo bayan ibtila'in da ya faɗa musu na Mabaliyar ruwa a yankunansu a Jigawa.
Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa (SEMA) ya ce zuwa yanzun adadin gawarwakin da aka tsamo ya kai 51.
Asali: Legit.ng