Matashin Da Ya Mayar Da Kwalin Digirinsa Jami'a Ya Samu Tallafin N500,000

Matashin Da Ya Mayar Da Kwalin Digirinsa Jami'a Ya Samu Tallafin N500,000

  • Mutumin da ya tayar da tarzoma a jami'ar da ya kammala karatunsa makon da ya gabata ya samu taimako
  • Matashin ya sanar da jama'a cewa yau ya samu tallafin kudi dubu dari biya (N500,000) daga hannun kungiya
  • Yan Najeriya a kafafen ra'ayi da sada zumunta sun tayasa murna kuma sun bashi shawari

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Oyo - Matashin da bidiyonsa ya bayyana makon jiya ya samu tallafin rabin milyan daya daga hannun kungiyar tsaffin daliban jam'iar Ladoke Akintola LAUTECH, Ogbomosho, Oyo.

Matashin mai suna Osunleke Alaba wanda ya karanci ilmin fitar da amfanin gona ya bayyana farin cikinsa bisa wannan gudunmuwa da ya samu.

Bayan kwanaki da bidiyonsa ya bayyana, Alaba ya aike sakon godiyarsa ga kungiyar tsaffin daliban jami'ar LAUTECH bisa wannan tallafi.

Yace:

"Ina mai amfani da wannan dama don bayyana godiyata ga kungiyar tsaffin daliban LAUTECH karkashin jagorancin Hon. Onilede Solomon wanda aka fi sani da LIMO, kwamitin amintattu da sashen kungiyar na jihar Oyo bisa bani Cheque na N500,000 yau."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Budewa Sanata Ubah Wuta, An Kashe Akalla Mutum 6

"Ina rokon Ubangiji ya cigaba da kasancewa da dukkan mambobin kungiyar bisa soyayyar da suka nuna min. Na gode."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alaba
Matashin Da Ya Mayar Da Kwalin Digirinsa Jami'a Ya Samu Tallafin N500,000 Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Dalilin Da Ya Sa Koma Makarantar Da Nayi Digiri Nace Su Dawo Min Da Kudi Na

Alaba ya bayyana cewa shine mutumin da aka gani cikin bidiyo ya je jami'ar fasahar Ladoke Akintola University (LAUTECH) ya tada tarzoma.

Legit ta kawo muku labarin wannan matashi da ya shiga makarantar da ya kammala karatun digirinsa inda ya bukaci su amshi kwalinsu su dawo masa da kudaden makarantar da ya biya tsawon shekarun da yayi a jami'ar.

A cewarsa:

"Na karbi kwali ne amma bata amfanar da ni komai ba. Na ji kebura a rayuwar nan amma dama daya dana samu shine inyi asirin kudi amma ba zan yi ba."
"Na bukaci mahaifi ne ya taimaka min da wasu kudade don in nemi abin yi. Ni dan wasan nishadi ne. Na samu lambobin girma da dama lokacin bautar kasa NYSC a 2016. Amma yace min bashin da ya karba don biyan kudin makarantana har yanzu bai gama biya ba."

Kara karanta wannan

Dabara: Yadda dalibai ajin karshe a likitanci ya koma mai siyar da abinci saboda yajin aikin ASUU

"Wata rana har ce min yayi da yiwuwan idan suka mutu sai na karbi bashi zan iya jana'izarsu. Sai da nayi kuka ranar."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel