Kotu Ta Baiwa Hukumar DSS Ikon Cigaba da Rike Tukur Mamu Tsawon Watanni 2
- Hukumar DSS ta shigar da kara kotu don a bata daman cigaba da rike Tukur Mamu don kammala bincike
- Jami'an hukumar DSS sun tsare Tukur Mamu a hannun tun makon da ya gabata kan wasu zarge-zarge
- Tukur Mamu ya kasance mai taimakawa wajen cinikin kudin fansa tsakanin yan bindiga da iyalan wadanda suka sace
Abuja - Babbar kotun tarayya dake zaman a birnin tarayya Abuja ta baiwa hukumar tsaron farin kaya DSS izinin cigaba da tsare Tukur Mamu, na tsawon watanni biyu.
Hukumar DSS a ranar 12 ga Satumba ta bukaci kotu ta bata damar kammala bincikenta kan Mamu.
A karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1617/2022 lauyan DSS, Ahmed Magaji, ya bukaci karin kwanaki 60.
Alkali Nkeonye Maha, a hukuncin da yanke ranar Talata, 13 ga Satumba, ya baiwa DSS daman cigaba da tsareshi, rahoton TheNation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Damke Tukur Mamu
Jami'an tsaron birnin Kahira a kasar Masar sun damke mai kokarin sulhu tsakanin yan bindiga da iyalan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna tare da iyalansa.
Tukur Mamu na hanyarsa ta tafiya kasar Saudiyya gudanar da Ibadar Umrah yayinda aka tsareshi a tashar jirgin Kahira na kwana guda.
Dirarsa jihar Kano ke da wuya, jami'an DSS suka same damkeshi kuma suka garzaya da shi ofishinsu.
Daga baya suka shiga gidansa da ofishinsa dake Kaduna suka shiga lalube. Sun yi ikirarin cewa sun samu kudade da kayan Sojoji.
Sakamakon Binciken da Muka Gudanar Kan Tukur Mamu Yana Da Daure Kai, DSS
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta ce sakamakon binciken da ta gudanar kan Tukur Mamu akwai ban mamaki sosai, Daily Trust ta rahoto.
Da take martani ga furucin da shahararren malamin Musulunci mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi yayi, hukumar ta ce ba za ta bari ta shagaltu ba.
Gumi ya zargi DSS da aikata ta’addanci, yana mai kalubalantar rundunar yan sandan ta farin kaya da ta saki Mamu, wanda ya kasance hadiminsa ko kuma ta gaggauta gurfanar da shi a kotu.
Asali: Legit.ng