Abdullahi Haske: Matashin Biloniya Daga Jihar Adamawa Wanda Ba Kowane Ya Sansa Ba
- Abdullahi Haske ya kasance matashin dan Najeriya mai tashen kudi domin har ya kai matakin biloniya
- Matashin wanda ya kasance dan asalin garin Yola, jihar Adamawa shine babban manajan kamfanin AA & R Investment Group
- Sai dai kuma duk da wannan arziki da Allah ya yi masa, Haske mutum ne da sam baya nuna kansa hakan ne yasa ba kowane ya sansa ba
Najeriya - Allah ya albarkaci Najeriya da al’umma masu kwazo da jajircewa wajen neman na kai. Da yawa daga cikin wadannan yan Najeriya sun tara arzikin da har sun kai matakin biloniya.
Abdullahi Haske na daya daga cikin irin wadannan mutane sai dai sam shi yana tafiyar da lamuransa ne cikin sauki ba tare da nuna shi din wani mai arziki bane.
Ko shakka babu, Haske mai shekaru 35 na daya daga cikin matasa biloniya a Najeriya.
Sai dai kuma kasancewarsa matashi kuma mai ji da kudi, wasu mutane na yawan sukar tushen arzikinsa, jaridar Thisday ta rahoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A zahirin gaskiya, Haske na da asali mai kyau. Yana da iyaye wadanda suka shirya shi sosai a duniyar masu arziki da wadata.
Matashin wanda ya kasance haifaffen garin Yola, Jihar Adamawa ya karanci bangaren siyasa a jami’ar Abuja ya kuma mallaki digiri na biyu a bangaren tattalin arziki a makarantar koyon kasuwanci na Lagas.
Wannan karatu da ya yi da wasu da dama sun bashi damar sanin kan kasuwanci tare da yin nasara a cikinta.
Ya yi aiki a matsayin dan kwangila tare da kamfanonin mai, gas, na gine-gine da kuma na gwamnati.
Kasancewarsa haziki, ba a dauki lokaci ba Haske ya zama babban manajan kamfanin AA & R Investment Group Vangudar ta rahoto.
Tun daga nan ne matashin ya dunga fadi tashi a duk wuraren da ya san zai karfafa kansa a kasar.
“N758,000 Nake Samu Duk Wata”: Matashi Dan Najeriya Da Ke Zaune A UK Ya bayyana Albashinsa Da Sauran Abubuwa
A wani labarin, wani dan Najeriya da ke zaune a UK ya ce mutanen da ke barin kasar a yanzu haka za su gamu da tsadar rayuwa da ke faruwa a chan.
A cewar mutumin mai suna Jaja, mutanen da ke zaune a UK yanzu haka suna fama ne da tsadar rayuwa.
Jaja wanda ya mallaki digirin digirgir, ya sha cacca daga wajen wani mai amfani da Twitter @_Nache_1, wanda ya zarge shi da yawan korafi ba tare da ya bayyana yawan kudin da yake samu ba.
Asali: Legit.ng