Kotun Daukaka Kara Ta Rage Zaman Yunusa Yellow A Gidan Yari, Bayan Zabe Za'a Sakoshi
- Kotun daukaka kara ta yi rangwame kan hukuncin shekaru 26 da aka yankewa Dahiru Yunusa Yellow
- Kotun dake jihar Rivers tace duk da cewa ta amince Yellow ya aikata laifin da ake zarginsa da shi, an rage zuwa shekaru 7
- An damke Inusa Yellow ne bisa laifin daukar yarinya daga garin Bayelsa zuwa Kano da kuma dirka mata ciki
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kotun daukaka kara dake zamanta a Fatakwal ta saukake hukuncin zaman shekaru 26 da babbar kotun tarayya dake Yenagoa Bayelsa ta yanke kan Yunusa Dahiru Yellow a Mayun 2020.
Kotun ta rage adadin shekarun daga 26 zuwa Bakwai, rahoton DailyNigeria.
A baya kun ji cewa Alkali Jane Inyang ta yankewa Yunusa Yellow hukuncin zaman shekaru 26 a gidan yari kan laifin safarar yarinya Ese Oruru da jima'i da ita.
Sakamakon haka lauyoyin Yunusa suka daukaka kara.
Lauyoyin sun hada da Abdul Mohammed, SAN, Yusuf Dankofa, Huwaila Mohammed, Sunusi Musa da Kayode Olaosebikan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kwamitin Alkalan karkashin jagorancin JS Iykegh ya yi watsi da daukaka karar amma ya amince shekaru 26 da aka yankewa Yunusa Yellow ya yi yawa kuma ya sabawa doka.
Alkalan suka ce duk da sun amince Inuwa Yellow ya aikata laifin kuma sun tabbatar da hukuncin babbar kotun tarayya, yanzu za'a rage zaman gidan yarin zuwa shekaru 7.
Sakamakon haka, za'a fara kirgen zaman gidan yarin Inusa Yellow daga ranar 25 ga Oktoba 2018 da aka fara gurfanar da shi kuma zai fito a Mayun 2023.
Kada Ku Mayar Dani Najeriya, Abba Kyari Zai Iya Kasheni: Hushpuppi Ya Roki Kotun Amurka
A wani labarin kuwa, shahrarren dan damfarar yanar gizo, Ramon Abbas, wanda akafi sani da Hushpuppi ya ce dakataccen dan sanda Abba Kyari na iya kasheshi idan gwamnatin Amurka ta mayar da shi Najeriya.
Hushpuppi ya bayyanawa kotun birnin California cewa tona asirin Abba Kyari da yayi ba karamin hadari ne ga rayuwarsa ba yanzu idan ya koma Najeriya bayan zama a gidan kurkuku a Amurka.
Asali: Legit.ng