Majalisar Dokoki Ta Bukaci a Dakatar da Shugabannin Kananan Hukumomi 15
- Majalisa dokokin jihar Neja zata dakatar da shugabannin ƙananan hukumomi 15 domin gudanar da bincike kan ciyo bashi
- Shugaban kwamitin binciken, Madaki Bosso, yace sun gano wasu Ciyamomi sun karɓo bashi ba tare da bin matakan doka ba
- Majalisa ta kafa kwmaitin ne domin gudanar da bincike kan yadda Ciyamomi ke ciyo bashi a kananan hukumomi 25 dake faɗin jihar
Niger - Kwamitin da majalisar dokokin jihar Neja ta kafa domin gudanar bincike kan yadda gwamnatocin kananan hukumomi ke ciyo bashi ya ba da shawarin a dakatar da Ciyamomi 15.
Jaridar Channels Tv ta ruwaito cewa hakan zai ba mambobin kwamitin damar shiga ko ina da bin kwakkwafi wajen sauke nauyin da aka ɗora musu yadda ya dace.
Da yake gabatar da rahoton kwamitin yayin zaman majalisa, shugaban kwamitin, Abdulmalik Madaki Bosso, ya bayyana sunayen ƙananan hukumomin da suke bukatar a dakatar da Ciyamominsu.
A bayaninsa, ƙananan hukumonin da abun ya shafa sun haɗa da Mokwa, Gbako, Suleja, Gurara, Tafa Paikoro, Bosso, Agwara, Borgu, Kontagora, Wushishi, Magama, Mariga, Mashegu, da kuma Rijau.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa, hakan ya yi dai-dai da sashi na 128 da 129 a kundin tsarin mulkin Najeriya 1999 wanda aka yi wa garambawul. Haka zalika yana kan layin sashi na 90 sakin layi A, B da C na kundin kananan hukumomi 2001 da aka yi wa kwaskwarima.
Meyasa kwamitin ke bukatar ɗaukar wannan matakin?
Madaki Bosso yayi zargin cewa mafi yawan dakatattun ciyamomin sun bi ta bayan fage sun kwamuso bashin ba tare da bin matakai ba, wanda a kalamansa majalisa ba zata lamurci haka ba.
A cewarsa, matsalar ta haifar da sabon tarnaƙi a kokarin tafiyar da gwamnatocin ƙananan hukumomi a faɗin jihar Neja.
Bugu da ƙaro, shugaban kwamitin binciken ya nemi a dakatar da zare miliyan N8m daga kuɗaɗen kananan hukumomi domin rage raɗaɗin bashi saboda gazawar ma'aikata na neman izinin majalisa.
Yace tsallake majalisa wajen ɗauke kuɗin daga asusun kowace ƙaramar hukuma ya saba wa sashi na 97 sakin layi na ɗaya a kundin dokokin ƙananan hukumomi 2021 wanda aka yi wa garambawul.
A wani labarin kuma Kotu Ta Soke Zaɓen Kananan Hukumomin Jihar Ebonyi Wanda Jam'iyyar APC Ta Lashe
A yau Alhamis, Babbar Kotun tarayya da ke zamanta a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi ta soke zaɓen kananan hukumomin da aka gudanar a faɗin jihar.
A cewar Kotun, zaɓen kananan hukumomin da ya gudana ranar 30 ga watan Yuli, 2022, ya saɓa wa tanadin sabon kundin dokokin zaɓen 2022.
Asali: Legit.ng