Gwamna Buni Ya Baiwa Iyalan Sheikh Goni Aisamu Kyautar Gidaje 3

Gwamna Buni Ya Baiwa Iyalan Sheikh Goni Aisamu Kyautar Gidaje 3

  • Gwamnan jihar Yobe ya cika alkawarin da ya yiwa iyalan Marigayi Sheikh Goni Aisami
  • Bayan samawa 'yayan marigayin biyu aiki, Mai Mala Buni ya baiwa matansa uku gida na kansu
  • Wasu jami'an Sojojin biyu a ranar 19 ga Agusta suka bindige Sheikh Aisami a Jaji-Maji

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe a ranar Laraba ya bada kyautar gidaje uku ga matan marigayi Sheikh Goni Aisami, babban malamin addinin da aka kashe a jihar.

Yayin mika takardar mallakan gidajen ga Sarkin Bade a Gashua, Abubakar Umar Suleiman, Gwamna Buni ya ce wannan cika alkawari ne da ya yiwa iyalan Malamin, rahoton PMNews.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin Ustaz Babagana Kyari, mai ba shi shawara kan harkokin addini, ya ce an baiwa matan gidaje ne don su kula da 'yayansu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Damke Tukur Mamu, mai sulhu tsakanin yan bindiga da fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna A Kasar Misra

Sarkin Bade ya mika godiyarsa ga gwamnan bisa wannan taimako da ya baiwa iyalan mamacin.

Wasu jami'an Sojojin biyu a ranar 19 ga Agusta suka bindige Sheikh Aisami a Jaji-Maji, yayinda ya rage musu hanya a mota.

Aisami
Gwamna Buni Ya Baiwa Iyalan Sheikh Goni Aisamu Kyautar Gidaje 3 Hoto: PMNews
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daya daga cikin 'yayan babban Malamin wanda ke aji biyu a jami'a, Abdullahi Goni Aisami, ya bayyana cewa yana da kanne takwas wadanda ke karatun firamare da sakandare.

Abdullahi ya tabbatar da labarin cewa gwamnatin jihar Yobe ta baiwa babban yayansa aiki bayan abinda ya faru.

Kalli hotunan gidajen

Aisami
Gwamna Buni Ya Baiwa Iyalan Sheikh Goni Aisamu Kyautar Gidaje 3
Asali: Facebook

Aisami
Gwamna Buni Ya Baiwa Iyalan Sheikh Goni Aisamu Kyautar Gidaje 3
Asali: Facebook

Aisami
Gwamna Buni Ya Baiwa Iyalan Sheikh Goni Aisamu Kyautar Gidaje 3
Asali: Facebook

Maganata Ta Karshe Da Mijina Yayinda Ya Hau Hanya, Uwargidar Sheikh Goni Aisami

Uwargidar Marigayi, Sheik Goni Aisami, Mallama Aisha ta bayyana maganarta ta karshe da tayi da babban Malamin yayinda yake hanya gab da ya dauki Sojan da yayi ajalinsa.

Kara karanta wannan

Wike: Babu Wanda Zai Iya Siya Na, Bana Kwadayin Mukamin Gwamnati

Mallama Aisha, wacce daya ce daga cikin matan Sheikh Aisami, ta ce wannan mumunan kisa da akayiwa maigidanta ya canza rayuwarsu gaba daya kuma an cucesu har abada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel