Mutum 43 Da Aka Sace A Masallacin A Zamfara Sun Samu Kubuta Bayan Biya Kudi, Daya Ya Mutu
- Masallata 43 cikin 44 da aka sace a Masallacin jihar Zamfara sun samu kubuta bayan kwanaki biyar
- Yan bindigan sun bautar da su cikin wadannan kwanaki inda suka tilastasu yin aiki a gonakinsu
- Majiyoyi sun bayyana cewa sai aka biya kudi milyan biyar da jarkunan man fetur matsayin fansa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Zamfara - Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sako Masallatan da suka sace a garin Zugu, karamar hukumar Bukkuyum makon da ya gabata.
Masallatan 44 da aka sace ranar Juma'a suna gabatar da Ibadah sun samu yanci ne bayan biyan kudin fansa N5m da jarkokin man fetur da aka kaiwa yan bindiga.
Majiyoyi sun bayyana cewa an sako su ne daren Talata misalin karfe 10:30 na dare, rahoton AIT.
Sun ce mutum 44 aka sace amma mutum daya ya mutu a hannun yan bindigan saboda firgici.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mutan garin suka taimaka wajen fito da mutanen kan babura daga cikin daji zuwa bakin hanya inda zasu samu motocin kaisu gida.
Karamar hukumar Bakura, Bukkuyi da Gummi na cikin kananan hukumomin da suka fi fuskantar barazanar yan bindiga a jihar Zamfara.
Hakan ya biyo bayan sulhun da gwamnatin jihar take ikirarin tayi da wasu manyan yan bindiga 9 a Magami da Dansadau.
Yan Bindiga Sun Toshe Hanyar Kaduna, Sun Kashe Mutum 2 Tare da Sace Matafiya Da Dama
A wani labarin mai kama da wannan, yan ta’adda sun toshe hanyar Birnin-Gwari zuwa Funtua, a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
A yayin harin, maharan sun kashe akalla mutum biyu ciki harda wani direba yayin da suka sace mutane da dama.
Shugaban kungiyar ci gaban masarautar Birnin-Gwari, Ishaq Kasai, ya bayyana a ranar Litinin, cewa yan ta’addan sun koma hanyar Birnin-Gwari Funtua inda suka toshe yankin sannan suka kashe wani direba da sace matafiya da dama.
Asali: Legit.ng