Jerin Jami'o'i 10 Da Suka Bijirewa ASUU, Basu Shiga Yajin Aiki Ba

Jerin Jami'o'i 10 Da Suka Bijirewa ASUU, Basu Shiga Yajin Aiki Ba

Akalla Jami'o'i guda goma 10) ba su shiga yajin aikin da kungiyar Malaman jami'oin Najeriya watau ASUU ta shiga ba tun watan Febrairu, 2022.

Jaridar Punch ta tattaro cewa kawo jiya Litinin, 5 ga watan Satumba 2022, ana karatu a wadannan jami'o'i.

Yau kwana ta 204 kenan da daliban jami'o'in Najeriya ke zaman gida sakamakon yajin aikin da malamansu suka shiga.

A yau Talata, Ministan Ilimi ya shirya zama da shugabannin jami'o'i don kawo karshen yajin aikin.

Ga Jerin jami'o'in da tun da farko basu shiga ba

1. Jami'ar Jihar Kwara

Kawo ranar Litinin, dalibai na cigaba da shiga aji suna karatu a jami'ar jihar Kwara. Daliban sun fara zana jarabawa tsawon makonni biyu da suka gabata

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

ASUU: An kai makura, gwamnatin Buhari ta yi sabon batu, ta fadi kokarinta a dinke matsalar ASUU

2. Jami'ar jihar Osun

Dalibai a jami'ar jihar Osun tun asali bas shiga yaji tare da kungiyar ASUU.

3. Jami'ar Chukuemeka Ojukwu dake Anambra

Jami'ar Ojukwu, mallakin gwamnatin jihar Anambra dake Igbariam bata shiga yajin aikin ki.

Jami'in hulda da jama'a na jami'ar, Dr Harrison Madubueze, ya bayyanawa Punch cewa ko kadan basu shiga yaji ba.

4. Jami'ar jihar Rivers

5. Jami'ar Ilimin Ajuru, Port Harcourt,

A Ignatius Ajuru University of Education, Port Harcourt, dalibai suna zana jarabawa.

Wani dalibin ajin karshe, Master Ovum Amadi, yace "Tuni yan aji biyu sun fara jarabawa."

Jihhi
Jerin Jami'o'i 10 Da Suka Bijirewa ASUU, Basu Shiga Yajin Aiki Ba
Asali: Twitter

6. Jami'ar Jihar Delta, DELSU

Jami'ar jihar Delta, Abraka, dalibai na karatunsu.

Shugaban ASUU na jami'ar, Farfesa Godin Demaki, yace shi da wasu lakcarori irinsa basu cikin malaman da suka bijirewa yajin aikin.

A cewarsa:

"DELSU na da Malamai 300 kuma kimanin 200 cikin ne mambobin ASUU."

7. Technical University Ibadan

Kara karanta wannan

Jami'ar Arewa ta yi watsi da ASUU, ta ce malamai su gaggauta dawowa bakin aiki

Jami'ar Technical, mallakin jihar Oyo tace babu ruwanta da ASUU.

8. Jami'ar jihar Legas

Jami'ar LASU babu ruwansu da yajin aikin ASUU saboda uwar kungiyar ta barranta da shugabanninta na jami'ar.

9. Jami'ar Ilimin jihar Legas

Hakazalika a jami'ar ilimin Legas dake Otto/Ijanikin, basu biyewa ASUU ba saboda ba a dade da kafasu ba.

Gwamnatin jihar Legas ta mayar da kwalejin ilimin Adeniran Ogunsanya da Kwalejin Micheal Otedola zuwa jami'a guda.

10. Jami'ar Jihar Akwa Ibom, Ikot-Akpaden

Wani malami a jami'ar yace da farko sun shiga yajin aikin amma suka janye bayan makonnin hudun farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida