Na Gaji da Najeriya Ne: Yaro Mai Shekaru 14 da Aka Tsinta a Filin Jirgin Sama
- Wani maraya mai shekaru 14 ya bayyana cewa ya gaji da kasar Najeriya kuma bashi da burin da ya wuce ya bar kasar nan kwata-kwata
- Yaron ya lallaba ta katangar hanyar Legas zuwa Abeokuta inda ya dire tare da kaucewa ma'aikata har ya shige fiffiken jirgin
- An same shi baya cikin hayyacinsa amma taimakon da ya samu na likitoci yasa ya farfado inda ake cigaba da bincike a kansa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Legas - Wani yaro mai shekaru 14 da aka tsintabaya cikin hayyacinsa a daya daga cikin jiragen Amurka dake filin sauka da tashin jiragen sama na Legas yace ya gaji da Najeriya kuma yana son barin kasar, ma'aikatan Bi-Courtney Aviation Services Limited, dake filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad suka ce.
Kamar yadda Channels TV ta rahoto, wata takarda da shugaban fannin yada labarai, Oluwatosin Onalaja a ranar Lahadi ya fitar, ya bayyana yaron da zama maraya daga jihar Kwara amma yana zama a yankin Badagry na jihar Legas.
"Wurin karfe 6:10 na ranar Lahadi, 4 ga watan Satumban 2022, kamfanin jirgin saman ya sanar da cewa an tsinta wani yaro mai shekaru 14 baya cikin hayyacinsa a daya daga cikin jiragen," takardar da Onalaja ya fitar ta bayyana.
Mai magana da yawun kamfanin yace yaron ya sanar da masu bincike cewa ya samu shiga wurin ta katangar hanyar Legas zuwa Abeokuta.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yace marayar ya shiga ya boye kansa a fuffuken jirgin. Ya ga "ma'aikata na aiki tare da sojojin sama amma ya boye tare da wucewa ta daji," takardar tace.
"An dauko yaron daga jirgin tare da kai shi asbitin filin sauka da tashin jiragen saman Murtala Muhamma domin a duba lafiyarsa. An mayar da shi asibitin sojin sama inda ya dawo hayyacinsa wurin karfe 10:20 na safe.
“Muna kokari a wurin binciken abinda ke faruwa domin tabbatar da abinda ya faru domin gujewa sake faruwar lamarin a gaba," Onalaja yace.
Kamar yadda takardar tace, an sallama yaron daga asibitin kuma an mayar da shi ofishin binciken laifuka na filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad tare da dogaran tsaro na Amurka domin amsa tambayoyi.
Buhari ya Kara Alawus din Tafiye-tafiye: 250% na Manyan Sakatarorin Gwamnati, 128% na Ministoci
A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammad Buhari ya amince da karin alawus din yawon aiki, DTA, ga ministoci, manyan sakatarorin gwamnati da ma'aikatan gwamnati daga mataki na 1 zuwa 17.
Alawus din yawon aiki, DTA, yana nufin kudin da gwamnati a ke biyan ma'aikacin da yayi tafiyar aiki.
Jaridar TheCable ta rahoto cewa, sabon amincewa da sabon alawus din ya bayyana ne a wata takarda mai kwanan wata 31 ga Augusta kuma an mika ta ne ga Ekpo Nta, shugaban hukumar albashi ta kasa.
Asali: Legit.ng