Jerin Sunayen Tsaffin Gwamnonin Najeriya 31 Da EFCC Ta Kama Tun Kafuwarta A 2003
- A kalla tsaffin gwamnoni 31 ne hukumar yaki da rashawa na EFCC ta kama kan zargin almundahar kudi daban-daban
- Gwamnoni ba za su kamu ba lokacin suna kan mulki saboda kariya da doka ta basu, don haka EFCC tana jira sai karshen wa'adinsu kafin ta kama su
- Sashi na 308 na kundin tsarin mulkin kasa na 1999, da aka yi wa kwaskwarima, ya bada kariya ga shugabanni don kare darajar ofishin
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'anatti, EFCC, tun kafuwarta a 2003 karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ta kama a kalla gwamnoni 30 a karshen wa'adinsu.
Bisa nazarin ayyukan hukumar, Legit.ng, ta tattaro muku adadin gwamnonin jihohi da hukumar ta kama tun kafuwarta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hukumar yaki da rashawar tana binciken laifuka ne masu alaka da kudi, mafi yawancin almundaha ko karkatar da kudade.
Gwamnan da aka kama a baya-bayan nan
Gwamnan da aka kama na baya-bayan nan shine Willie Obiano, tsohon gwamnan Jihar Anambra.
An kama Obiano ne nan take bayan ya rasa kariyar da doka ta bashi saboda sunansa na cikin jerin wadanda ake zargi da rashawa.
Mafi yawancin gwamnonin an zarge su ne da bada kwantiragin jihohinsu ba bisa ka'ida ba da karkatar da kudin gwamnati zuwa aljihunsu.
Sashi na 308 na kudin tsarin mulki na 1999, da aka yi wa kwaskwarima, ya bada kariya ga gwamnonin jihohi don wasunsu na da kasafi da ya fi na wasu kasashen Afirka.
Ga jerin sunayen tsaffin gwamnoni 30 da hukumar ta taba kamawa:
- Willie Obiano na Jihar Anambra
- James Ibori na Jihar Delta
- Rochas Okorocha na Jihar Imo
- Bukola Saraki na Jihar Kwara
- Orji Uzor Kalu na Jihar Abia
- Peter Ayodele Fayose na Jihar Ekiti
- Gabriel Suswam na Jihar Benue
- Audu Abubakar na Jihar Kogi
- Abdullahi Adamu na Jihar Nasarawa
- Aliyu Akwe Doma na Jihar Nasarawa
- Joshua Dariye na Jihar Plateau
- Jonah Jang na Jihar Plateau
- James Bala Ngilari na Jihar Adamawa
- Murtala Nyako na Jihar Adamawa
- Ali Modu Sheriff na Jihar Borno
- Danjuma Goje na Jihar Gombe
- Jolly Nyame na Jihar Taraba
- Sule Lamido na Jihar Jigawa
- Aliyu Wammako na Jihar Sokoto
- Abdulaziz Yari na Jihar Zamfara
- Theodore Orji na Jihar Abia
- Chimaroke Nnamani na Jihar Enugu
- Sullivan Chime na Jihar Enugu
- Ikedi Ohakim na Jihar Imo
- Godswill Akpabi na Jihar Akwa Ibom
- Diepreye Alamieyeseigha na Jihar Bayelsa
- Timipre Sylva na Jihar Bayelsa
- Lucky Igbinedion na Jihar Edo
- Olugbenga Daniel na Jihar Ogun
- Adebayo Alao-Akala na Jihar
- Rashidi Ladoja na Jihar Oyo
Asali: Legit.ng