Na Kashe Iyayena Saboda Suna Kirana Mahaukaci Don Ina Yabon Manzon Allah, Mawakin Tijjaniya Azzakiru Munkaila
- Mutumin da ya kashe iyayensa a jihar Jigawa ya bayyana cewa hukuncin haddi yayi musu saboda suna kiransa mahaukaci don ya kasance Azzakiru
- Mawakin yace shi Azzakirun darikar Tijjaniya ne kuma saboda hakan iyayensa ke nuna kiyayya ga Manzo Allah (SAW)
- Munkaila yace yayi imani za'a sakeshi saboda hukuncin gaskiya yayi kuma Allah na tare da mai gaskiya
Dutse - Matashin da ya kashe iyayensa a jihar Jigawa, Munkaila Ahmadu, ya bayyana dalilin da yasa ya hallaka iyayen da suka haifeshi da tabarya a karamar hukumar Gagarawa.
Munkail wanda Azzakiru ne, mawakin darikar Tijjaniyya yace iyayensa na kiransa mahaukaci kuma suna kalaman nuna rashin yarda da wakokin yabon Manzon Allah (SAW) da yake yi.
Premium Times ta ruwaito cewa Munkaila ya yi bayani a faifan bidiyo cewa ko kadan ba ya nadaman abinda yayi saboda ya yanke musu hukuncin wanda ya zagi Manzon Allah ne.
A cewarsa:
"Na kashesu ne saboda sun ki amincewa da gaskiya game da Manzon Allah (SAW). Na kashesu saboda hukuncin duk wanda ya zagi Manzon Allah kisa ne, kuma babu gafara ga wanda yayi haka."
"Na Azzakirun Manzon Allah, wannan shekarar nike da niyyar fito da bidiyon wakata kuma Idan Allah ya yarda zan yi hakan. Za'a sake ni saboda Allah na tare da mai gaskiya, shi yasa ko a jikina bana nadama."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Iyayena ba sa son Manzon Allah saboda ina yabonsa, sun ce ni mahaukaci ne, na roki mahaifi ne ya goya min baya, nace masa ba na neman mata, bana caca, ban shan kwaya, kuma ban sata, amma ya ki."
"Mahaifiyata har wajen makwabta take zuwa tana fadawa mutane ni mahaukaci ne saboda na ki zuwa gona."
Matashi Ya Doke Mahaifansa Da Tabarya Har Lahira A Jigawa, An Cafke Shi
A baya mun kawo muku cewa wani matashi dan shekara 37 mai suna Munkaila Ahmadu, ya halaka mahaifansa a kauyen Zarada-Sabuwa da ke karamar hukumar Gagarawa ta jihar Jigawa.
Adam ya ce Munkaila ya yi amfani da tabarya wajen doke mahaifinsa, Ahmad Muhammad mai shekaru 70 wanda shine hakimin kauyen da kuma mahaifiyar Hauwa Ahmadu mai shekaru 60.
Asali: Legit.ng