Abin Al'ajabi: Halittar Wani Yaro Mai Shudin Ido Ya Girgiza Intanet, Jama'a Na Ta Cece-kuce Kan Bidiyonsa

Abin Al'ajabi: Halittar Wani Yaro Mai Shudin Ido Ya Girgiza Intanet, Jama'a Na Ta Cece-kuce Kan Bidiyonsa

  • Yanayin halittar wani karamin yaro ya baiwa mutane da dama mamaki saboda abubuwan da yake dauke da su a fuskarsa
  • An haifi yaron da furfura a kansa, idanunsa suna da launin shudi sannan kuma yana da wani fashin haske kamar na tsawa shimfide a fuskarsa
  • Mabiya shafukan soshiyal midiya yaba kamanninsa yayin da wasu ke tunanin ba zai rasa wani rashin lafiya da ke damunsa ba

Bidiyon wani karamin yaro bakin fata dauke da idanu masu launin shudi da wasu hallita ta musamman ya haifar da cece-kuce a soshiyal midiya.

A cikin wani bidiyon TikTok da ya samu sama da mutane miliyan daya da suka kalla, yaron ya kalli cikin kamara yayin da aka hasko yanayin halittar fuskarsa mai ban mamaki.

Dan baiwa
Abin Al'ajabi: Halittar Wani Yaro Mai Shudin Ido Ya Girgiza Intanet, Jama'a Na Ta Cece-kuce Hoto: TikTok/@raoultsasa0
Asali: UGC

Baya ga idanu masu launin shudi da yaron ke dauke da su, yana kuma da furfura a gaban gashin kansa sannan akwai wani fashin haske kamar na tsawa shimfide a fuskarsa.

Kara karanta wannan

Babban gaye: Yadda nau'in takalmin wani dan kwalisa ya girgiza mutane a intanet

Zanen tsawar ya fara daga furfuran kansa sannan ya bazu har zuwa kan hancinsa ya gangara kan saman labbansa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jama’a sun yaba kyawun halitta na wannan yaro mai ban al’ajabi.

Kalli bidiyon a kasa:

D'Cee Killion Living ya ce:

“Kyakkyawan yaro. Kamar tsawa ne⚡️kan fuskarsa. Ya hadu matuka.”

Lunar Moon ta ce:

“Yana da kyau sosai. Ina ta tunanin hasken tsawa ne ya sumbace shi.”

Duc Nambouri ya ce:

“Ya yi daban a cikin mutane. Ba zai ya yi gwagwarmayar zama babban jarumi ba. Ya rigada ya yi zarra a cikin dandazon mutane.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng