Dan Shekara 15 Yaje Sayan Motar N36m, Mai Sayar Da Mota Ya Kira Yan Sanda

Dan Shekara 15 Yaje Sayan Motar N36m, Mai Sayar Da Mota Ya Kira Yan Sanda

  • Wani dan shekara 15 ya dira wajen dillalan mota don sayar sabuwar mota wanda kudinta ya kai N36m
  • Mai sayar da motoci da wuri ya kira yan sanda don tabbatar da cewa da kudin halal ya zo saya
  • Daga baya maganar da yaron yayi musu ya baiwa jami'an tsaron mamaki sosai, yace likitoci sunce shekaru 5 kacal suka rage masa a duniya

Wani dan shekara 15 mara lafiya ya shiga shagon sayar da motoci don sayan wata tsaleliyar mota mai tsada.

Temmyy, wanda ya daura labarin a shafinsa na Tuwita yace yaron ya shiga cinikin motar da kudinta ya kai N36million.

Mai sayar da motar ya gaggauta kiran hukuma. Yayin yiwa yaron tambayoyi, sai ya bayyana cewa shekaru biyar kadai ya rage masa a duniya saboda haka a barshi ya ci rayuwarsa kan ya mutu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Hotunan Jana'izar Mutune 7 Yan Gida Ɗaya Da Suka Rasu Bayan Sunyi Karin Kumallo Da Dambu A Sokoto

Car 15
Dan Shekara 15 Yaje Sayan Motar N36m, Mai Sayar Da Mota Ya Kira Yan Sanda Hoto: Momo productions / Martyn Lucy
Asali: Getty Images

A cewarsa, wannan jawabi ya baiwa jami'an tsaron tausayi kuma hakan yasa suka rabu da shi ya sayi abinda yake so.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Temmyy yace:

"Wani direban ya bada labarin wani dan shekara 15 da ya gani a shagon abokinsa yaje sayan mota. Yace yaron ya shigo cinikin motar N36M kuma ya shirya biya kai tsaye."
"Gudun abinda ka iya biyo baya, sai dilan motan ya kira yan sanda; isowarsu ke da wuya suka fara masa tambayoyi don sanin ko kudin mahaifinsa ne ko yayansa."

A cewar Direban, yaron ya fada musu cewa:

"Ya kuke damuna ne? Shekaru biyar kadai suka rage min a duniya; ku bar ni inji dadin rayuwata."

Asali: Legit.ng

Online view pixel