An Damke Tsohon Soja Yana Kaiwa Yan Bindiga Makamai A Zamfara

An Damke Tsohon Soja Yana Kaiwa Yan Bindiga Makamai A Zamfara

  • Jami'an tsaro sun damke wani Soja da ajiye aiki bara ya koma kaiwa yan bindiga makamai a Arewa
  • Tsohon Sojan dan asalin jihar Zamfara ne kuma yana kai bindiga kusan dukkan jihohin Arewa maso yamma
  • Ya bayyana cewa N200,000 zuwa N300,000 ake biyansa kai bindigan sayarwa wajen yan ta'adda

Gusau - Jami'an hukumar yan sanda a jihar Zamfara sun damke wani tsohon Soja da wani kasurgumin dan bindiga masu kaiwa yan bindiga makamai a jihar.

Sojan mai suna, Saidu Lawal, ya kasance cikin yan bindigan da suka addabi jihohin Neja, Kaduna, Katsina, Kebbi da Kaduna.

An damkeshi ne a titin Kaduna zuwa Abuja dauke da makamai biyu zai kaiwa wani dan bindiga mai suna, Dogo Hamza, a Tsafe jihar Zamfara.

Sa'idu wanda ya ajiye aikin Soja a shekarar 2021 ya kasance mai kaiwa yan bindiga makamai, cewar Kakakin hukumar yan sandan jihar, Mohammed Shehu, rahoton ChannelsTV.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mai Magana da Yawun Rundunar 'Yan Sanda a Najeriya Ya Mutu

Saidu
An Damke Tsohon Soja Yana Kaiwa Yan Bindiga Makamai A Zamfara Hoto: @channelsTV
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A jawabin da ya fitar a Gusau, yace:

"A ranar 27 ga Agusta, 2022 misalin karfe 1730hrs, jami'an hukumar yan sanda sun samu labarin da ya kai ga damke wani tsohon Soja da yayi aik a 73 Batallion Army Barrack Kano."
"An damkeshi cikin mota kirar Pontiac Vibe mai lamba KRD 686 CY Lagos, a hanyar Abuj-Kaduna ya nufi Zamfara. An bincikesa kuma aka kama makamai."
"Yayin yi masa tambayoyi, ya ce ya dauko makaman ne daga karamar hukumar Loko ta jihar Nasarawa zuwa wajen kwastomansa, Dogo Hamza a kauyen Bacha, karamar hukumar Tsafe, jihar Zamfara."
"Ya bayyana cewa ya dade yana kai makamai wa yan bindiga a Kaduna, Katsina, Neja da jihar Kebbi."

Daga cikin makaman da aka kwace hannunsa akwai bindigogin AK-47 guda biyu, magazaine 8 da harsasai 501.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida