Jerin Shahrarrun Kasashen Duniya 11 Masu Shugabanni Kasa Mata

Jerin Shahrarrun Kasashen Duniya 11 Masu Shugabanni Kasa Mata

Yayinda Maza ke jagorantar yawancin kasashen duniya a tarihi, Mata sun fara mamaye kujerun shugaban kasa da manyan mukamai a duniya.

Wadannan Mata na shan yabo a fadin duniya bisa irin jagorancin da sukeyi a kasashensu.

Ga jerin wasu kasashe masu shugaba mace:

1. Nepal

An zabi Bidya Devi Bhandari matsayin shugabar kasar Nepal ranar 29 ga Oktoba 2015. Ita ce mace ta farko da ta zama shugabar kasar jihar.

A baya ta kasance Mininstan Muhalli a 1997, sannan tayi Ministar Tsaro a shekarar 2009 zuwa 2011.

2. Taiwan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da sa'insar dake gudana tsakanin Taiwa da Sin, Tsai Ing-wen ta kasance shugabar kasar tun daga ranar 20 ga Mayu, 2016. Itace mace shugabar kasa ta farko a tarihin kasar.

Kara karanta wannan

Manyan 'Yan Ta'adda 8 Sun Shiga Hannun Dogaran Fadar Shugaban Kasa a Abuja

3. Singapore

Halimah Yacob ta zama shugabar kasar Singapore ranar 14 ga Satumba 2017. Itace mace shugabar kasa ta farko a tarihin kasar.

Ta kasance tsohuwar Kakakin Majalisar dokokin jihar.

4. Trinidad and Tobago

Paula Mae Weekes, na jagorantar al'ummar kasar tun bayan lashe zabe ranar 19 ga Maris, 2018.

5. Georgia

An zabi Salome Zourabichvili matsayin shugabar kasar Georgia ranar 16 ga Satumba, 2018.

Jacinda
Jerin Shahrarrun Kasashen Duniya 7 Masu Shugabanni Kasa Mata
Asali: AFP

6. Moldova

Moldova wata kasa ce dake gabashin Turai. Tana da Shugaba Maia Sandu tun bayan nasara a zaben ranar 24 ga Disamba 2020.

Itace mace shugabar kasa ta farko a tarihin kasar.

7. Slovakia

Zuzana Caputova ta zama shugabar Slovakia ranar 15 ga yuni 2019. Har yanzu tana kan mulki.

8. Greece

An zabi Katerina Sakellaropoulou matsayin shugabar kasar Greece ranar 13 ga Maris, 2020.

A baya ta kasance shugabar kotun kolin kasar.

9. Barbados

Sandra Mason, shugabar kasar Barbados bayan samun yancin kan kasar daga wajen Birtaniya.

Kara karanta wannan

Magidanci Mai Mata 4 Da 'Yaya 34 Sun yi Rijistan Zabe, Yace Atiku Duk Zasu Kadawa Kuri'u

Ta zama shugaban kasa ranar 20 ga Oktoba, 2021.

10. Honduras

An zabi Xiomara Castro matsayin shugabar kasar Honduras ranar 27 ga Junairu, 2021.

Mijinta ya kasance shugaban kasar a baya amma ya fuskanci juyin mulki a 2009. Daga baya aka gabatar da ita matsayin yar takara kuma tay nasara a 2021.

11. New Zealand

Jacinda Kate Laurell Ardern shahrarriyar yar siyasa ce wacce ke mulkin New Zealand.

Ta sha yabo daga wajen kasashen duniya bisa yadda ta takaita matsalar kashe Musulmai a kasar

Hakazalika yadda ta taimakawa kasar lokacin annobar Korona.

Asali: Legit.ng

Online view pixel